ukarofi

12479 Posts
Man United ta miƙa wa Bruno Fernandes tayin tsawaita kwantiragi har zuwa 2029

Man United ta miƙa wa Bruno Fernandes tayin tsawaita kwantiragi har zuwa 2029

ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta miƙa wa kyaftin ɗinta, Bruno Fernandes, sabuwar yarjejeniyar kwantiragi da za ta iya ci gaba da riƙe ɗan wasan ƙasar Portugal a Old Trafford har zuwa shekarar 2029. Matakin na nuna irin muhimmancin da kulob ɗin ke bai wa Fernandes, yayin da Manchester United ke ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da kuma dawo da ita kan turbar fafutukar lashe manyan kofuna a ƙwallon ƙafar Ingila. Fernandes ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan Manchester United tun bayan komawarsa kulob ɗin daga Sporting Lisbon a watan Janairun 2020, inda cikin kankanin lokaci ya zama ɗaya…
Read More
FIFA ta ƙi amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na NFF

FIFA ta ƙi amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na NFF

Sabbin bayanai sun nuna cewa Hukumar Kula da ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ba ta amince da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da aka gabatar domin tafiyar da harkokin Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ba. Haka kuma, FIFA ba ta amince da sunayen mambobin da za su kasance cikin irin wannan kwamiti ba, kamar yadda wasu majiyoyi masu inganci da ke da masaniya kan lamarin suka tabbatar. Majiyoyin sun ce a wani taro da jami’an FIFA suka gudanar da wakilan Gwamnatin Nijeriya da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya a birnin Zurich na ƙasar Switzerland, hukumar ta FIFA ta saurari bayanai…
Read More
Manoma ba su san an raba takin tallafi a Gaya ba — Sarkin Noman Gaya

Manoma ba su san an raba takin tallafi a Gaya ba — Sarkin Noman Gaya

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Sarkin Noman Gaya, Alhaji Bello Abubakar, ya bayyana cewa manoman da ke ƙaramar Hukumar Gaya ba su amfana da tallafin takin da gwamnatin jihar ta ce ta raba domin bunƙasa harkar noma ba. Ya ce duk da cewa an bayyana cewa an kai takin tallafi har kimanin tireloli biyu zuwa Gaya, su a matsayinsu na wakilan manoma ba su san lokacin da aka raba takin ba. “An raba taki har ya kai tireloli biyu a Gaya, amma mu ba mu san lokacin da aka raba shi ba,” in ji Sarkin Noman. Alhaji Bello ya…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Warawa ya karɓi sama da mutum 500 daga PDP da NDC

Shugaban ƙaramar hukumar Warawa ya karɓi sama da mutum 500 daga PDP da NDC

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Warawa, Alhaji Lamido Sunusi Ahmad, ya karɓi sama da mutum 500 da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun PDP da NDC zuwa Jam’iyyar APC. An karɓi sabbin mambobin jam’iyyar ne daga mazabar Garin Dau, a wani taro da aka gudanar a gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke Garin Dau a ranar Talata. Da yake karɓar masu sauya sheƙar, Alhaji Lamido Sunusi Ahmad ya bayyana ranar a matsayin mai matuƙar muhimmanci a gare shi. Ya ce kusan kullum ana samun mutanen da ke barin wasu jam’iyyu domin shiga APC, sakamakon yadda Shugaban ƙasa…
Read More
2027: Mun yi shiri tsaf domin nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf — APC Ungogo

2027: Mun yi shiri tsaf domin nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf — APC Ungogo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma shugaban Karta Kwana na Ilimi a ƙaramar Hukumar Ungogo, Alhaji Sammani Muhammad Abdulmumin Zango, ya ce sun yi shiri tsaf domin tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamnan Jihar Kano na shekarar 2027, da yardar Allah. Alhaji Zango ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce zuwa yanzu alamu sun nuna cewa al’ummar Jihar Kano, maza da mata, musamman masu kaɗa ƙuri’a, suna tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf kuma za su sake zaɓensa a shekarar 2027. “Dalilin hakan…
Read More
Dan Ministan Ayyuka, David Umahi ya zama Shugaban ƙaramar Hukuma a Ebonyi

Dan Ministan Ayyuka, David Umahi ya zama Shugaban ƙaramar Hukuma a Ebonyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dan Ministan Ayyuka na Tarayya kuma tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi, Sanata David Umahi, mai suna Osborn Nweze Umahi, an rantsar da shi a matsayin Shugaban ƙaramar Hukumar Ohaozara da ke Jihar Ebonyi. Osborn Umahi mai shekara 28 ya yi rantsuwar kama aiki ne a ranar Talata, bayan nasarar da ya samu a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Ebonyi da aka gudanar ranar 22 ga Agusta, 2026, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC. Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ne ya rantsar da sabon shugaban ƙaramar hukumar, a wani biki da ya samu halartar manyan…
Read More
2027: Idan na ci zaɓe zan dawo wa da ƙananan hukumomi kuɗaɗen su kai tsaye – Atiku 

2027: Idan na ci zaɓe zan dawo wa da ƙananan hukumomi kuɗaɗen su kai tsaye – Atiku 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin aiwatar da hukuncin Kotun ƙoli kan 'yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. A ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa ya kamata a rika biyan kudaden da ake warewa kananan hukumomi 774 daga Asusun Tarayya kai tsaye zuwa gare su. Hukuncin ya biyo bayan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan gwamnonin jihohi 36 game da yadda ake gudanar da harkokin kananan…
Read More
Makusanta sun nuna gamsuwa da naɗa ƙadiri sarautar Oshi-Ozoya a Kano

Makusanta sun nuna gamsuwa da naɗa ƙadiri sarautar Oshi-Ozoya a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano ’Yan uwa da abokan arziki sun nuna gamsuwa tare da bayyana farin cikinsu kan naɗa Muhammad Abdulkadir, FCA, sarautar Oshi-Ozoya na al’ummar Edo mazauna Jihar Kano. An bayyana hakan ne yayin wani taron taya shi murnar samun wannan sarauta da aka gudanar a wani ɗakin taro da ke kan Lodge Road a Kano. Da take jawabi a wajen taron, Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana Kano a matsayin gida ga duk wani ɗan Nijeriya mai son zaman lafiya da bin doka da oda. Ta ce Muhammad Abdulkadir mutum ne da ya kasance yana bayar…
Read More
Taron tsofaffin ɗalibai ana shirya shi ne domin ƙarfafa zumunci — MK Rano

Taron tsofaffin ɗalibai ana shirya shi ne domin ƙarfafa zumunci — MK Rano

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Mai magana da yawun ƙungiyar Tsofaffin Daliban Tsohon Kwalejin Horar da Malamai da ke Wudil, Ambasada M. K. Adam Rano, ya bayyana cewa tarukan ƙungiyoyin tsofaffin dalibai na makarantu ana shirya su ne domin sada zumunci da ƙarfafa alaƙa tsakanin abokan karatu. Rano ya bayyana hakan ne yayin bikin cikar shekaru 35 da kafa ƙungiyar, wanda aka gudanar a ɗakin motsa jiki na tsohuwar kwalejin da ke Wudil a makon da ya gabata. Ya ce babban makasudin shirya taron shi ne bikin cikar ƙungiyar shekaru 35 da kuma bai wa tsofaffin daliban damar sake…
Read More
Makarantar St. Louis ta yi walimar saukar Alƙur’ani karo na 21 a Kano

Makarantar St. Louis ta yi walimar saukar Alƙur’ani karo na 21 a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Makarantar ’yan mata ta St. Louis da ke Kano ta shirya walimar saukar Alƙur’ani Mai Girma karo na 21, inda ɗalibai 47 suka kammala karatun Alƙur’ani. Makarantar, wadda ta cika shekaru 75 da kafuwa, ta gudanar da taron ne domin taya ɗaliban murnar wannan gagarumar nasara. Mataimakiyar shugaban makarantar, Malama Halima Baba Yaro, ta bayyana a wajen taron cewa makarantar tana da tsari na musamman wajen koyar da Alƙur’ani Mai Girma da kuma ilimin addini. Ta ce manufar wannan tsari ita ce bai wa ɗalibai damar fahimtar addini tare da samun kyakkyawar tarbiyya da sanin…
Read More