ukarofi

12477 Posts
Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya ziyarci rundunar ’yan sandan Kano gabanin zaɓen 2027

Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya ziyarci rundunar ’yan sandan Kano gabanin zaɓen 2027

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta karɓi baƙuncin wata tawaga daga Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa (National Peace Committee), ta hannun Sakatariyar Cibiyar Kukah, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Tawagar ta ziyarci rundunar ne a ranar Talata, 1 ga Satumbar 2026, ƙarƙashin jagorancin Mista Espom Ajanya, ƙaramin Manajan Shirye-shirye na Cibiyar Kukah, wadda ke aiki a matsayin Sakatariyar Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa. Da yake jawabi yayin ziyarar, Ajanya ya ce tattaunawar na daga cikin shirye-shiryen Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa gabanin babban zaɓen…
Read More
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 1,487, sun ceto mutane 777 cikin watanni biyu

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 1,487, sun ceto mutane 777 cikin watanni biyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shalkwatar Tsaron Nijeriya (DHƙ) ta ce rundunar sojin ƙasar ta gudanar da ayyukan tsaro 7,062 a faɗin ƙasar cikin watannin Yuli da Agusta, inda ta hallaka ’yan ta’adda da ’yan tawaye 1,487 tare da ceto mutane 777 da aka yi garkuwa da su. Daraktan Yaɗa Labarai na Shalkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja yayin taron haɗin gwiwa na hukumomin tsaro. Ya ce ayyukan sojin sun haɗa da na ƙasa, sama da ruwa, inda aka mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da…
Read More
Nijeriya ta kama bindigogi 204 da aka ɓoye a cikin kwantena a tashar jirgin ruwan Legas

Nijeriya ta kama bindigogi 204 da aka ɓoye a cikin kwantena a tashar jirgin ruwan Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta ce ta kama bindigogi kirar pump-action 204 da aka ɓoye a cikin wani kwantena da ya isa tashar jirgin ruwa ta TinCan Island da ke Legas daga ƙasar Turkiyya. An ɓoye makaman ne a tsakanin kayayyakin gida kamar kujeru, firinjoci, na'urorin hasken rana da kuma garin sabulu. Jami'an kwastam sun ce sun gano su ne bayan bayanan sirri da suka samu suka sa aka yi cikakken bincike kan kwantenan. Hukumar ta bayyana cewa bindigogin nau'in MAS 49 Alter Magnum pump-action rifles ne, kuma an gano wasu kayayyakin bindiga tare…
Read More
Gwamna Yusuf ya jagoranci tawaga mai ƙarfi zuwa tarukan Mauludi a Kano

Gwamna Yusuf ya jagoranci tawaga mai ƙarfi zuwa tarukan Mauludi a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi zuwa tarukan Mauludin Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a sassa daban-daban na jihar, a wani mataki da ya ƙara nuna muhimmancin da gwamnatinsa ke bai wa hulɗa da malaman addinin Musulunci da al’ummomin jihar. Gwamnan ya bar Fadar Gwamnatin Jihar Kano da misalin ƙarfe 10:00 na dare, inda ya fara rangadin tarukan Mauludi daban-daban tare da ci gaba da ziyartar wurare har tsawon dare, kafin ya dawo Fadar Gwamnatin da misalin ƙarfe 7:02 na safiya. A cikin wannan rangadi na dare,…
Read More
An yi kira ga Gwamnan Katsina ya ɗauki matakin gaggawa kan yanayin tsaro a Funtua

An yi kira ga Gwamnan Katsina ya ɗauki matakin gaggawa kan yanayin tsaro a Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua Kwamred Mannir Suleiman ya yi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da ya ɗauki mataki na gaggawa domin kawo ƙarshen hare haren 'yan bindiga a yankin Funtua musamman a cikin garin Funtua. Kwamred Suleiman ya yi wannan kira a hira da manema labarai a Katsina, ya nuna damuwa a cikin mako biyu irin mummunar hare haren da 'yan bindiga ke kai wa da ya yi sanadiyar rasa rayuka, jikkata jama'a da satar dabbobi. "Sun kai hare hare a Kasuwar Mata, Unguwar Dahiru, Kasuwar Madalla Sokoto Bypass da Jabiri in da nan ma…
Read More
Amusan, Ezekiel da Ajayi za su wakilci Nijeriya a gasar ƙarshe ta Diamond League ta 2026

Amusan, Ezekiel da Ajayi za su wakilci Nijeriya a gasar ƙarshe ta Diamond League ta 2026

Nijeriya za ta samu wakilci daga ’yan wasanta uku, Tobi Amusan, Nathaniel Ezekiel da Kayinsola Ajayi, a gasar ƙarshe ta Diamond League ta shekarar 2026 da za a gudanar a birnin Brussels na ƙasar Belgium. Za a gudanar da gasar ta shahararriyar ƙungiyar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya na tsawon kwanaki biyu, daga ranar 4 zuwa 5 ga Satumba, inda manyan ’yan wasa daga sassa daban-daban na duniya za su fafata a fafatawar ƙarshe ta kakar gasar ta bana. Amusan, wadda ke cikin fitattun ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Nijeriya, za ta nemi rufe kakar wasanninta da kyakkyawan…
Read More
Anthony Joshua da Tyson Fury za su goge raini a Amurka

Anthony Joshua da Tyson Fury za su goge raini a Amurka

Tsohon zakaran damben ajin masu nauyi na duniya, Tyson Fury, ya tabbatar da cewa an kusa cimma matsaya kan fafatawar da aka daɗe ana jira tsakaninsa da ɗan damben Birtaniya ɗan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, inda aka tsara gudanar da damben a filin Madison Sƙuare Garden da ke birnin New York na Amurka. Fury ne ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram, inda ya wallafa hoton tallata damben da ke nuna shi da Joshua a gaban hoton gine-ginen birnin New York. Sai dai bai bayyana takamaiman ranar da za a yi damben ba. Fury ya rubuta cewa, “Wane irin wuri…
Read More
An tsare matashi ɗan shekaru 18 kan zargin shirya sace Mbappe

An tsare matashi ɗan shekaru 18 kan zargin shirya sace Mbappe

Hukumomin shari’a a Faransa sun sanya wani matashi mai shekaru 18 a ƙarƙashin bincike na hukuma, bisa zargin hannu a jerin hare-haren kutsawa gidaje da ƙarfi da kuma shirye-shiryen sace attajirai, ciki har da ɗan wasan Real Madrid da tawagar Faransa, Kylian Mbappe. Jaridar Le Parisien ta Faransa ta ruwaito cewa an gurfanar da matashin, wanda aka bayyana sunansa da Clement L., tare da wani da ake zargi abokin aikinsa, a ranar 21 ga Agusta a Nanterre, da ke Hauts-de-Seine, kan zargin aikata laifukan fashi cikin tsari na ƙungiya. Rahotanni sun ce masu bincike na zargin matashin da kasancewa wanda…
Read More
Man United ta miƙa wa Bruno Fernandes tayin tsawaita kwantiragi har zuwa 2029

Man United ta miƙa wa Bruno Fernandes tayin tsawaita kwantiragi har zuwa 2029

ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta miƙa wa kyaftin ɗinta, Bruno Fernandes, sabuwar yarjejeniyar kwantiragi da za ta iya ci gaba da riƙe ɗan wasan ƙasar Portugal a Old Trafford har zuwa shekarar 2029. Matakin na nuna irin muhimmancin da kulob ɗin ke bai wa Fernandes, yayin da Manchester United ke ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da kuma dawo da ita kan turbar fafutukar lashe manyan kofuna a ƙwallon ƙafar Ingila. Fernandes ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan Manchester United tun bayan komawarsa kulob ɗin daga Sporting Lisbon a watan Janairun 2020, inda cikin kankanin lokaci ya zama ɗaya…
Read More
FIFA ta ƙi amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na NFF

FIFA ta ƙi amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na NFF

Sabbin bayanai sun nuna cewa Hukumar Kula da ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ba ta amince da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da aka gabatar domin tafiyar da harkokin Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ba. Haka kuma, FIFA ba ta amince da sunayen mambobin da za su kasance cikin irin wannan kwamiti ba, kamar yadda wasu majiyoyi masu inganci da ke da masaniya kan lamarin suka tabbatar. Majiyoyin sun ce a wani taro da jami’an FIFA suka gudanar da wakilan Gwamnatin Nijeriya da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya a birnin Zurich na ƙasar Switzerland, hukumar ta FIFA ta saurari bayanai…
Read More