ukarofi

12476 Posts
Gwamnatin Tarayya ta umarci jami’o’i, kwalejojin fasaha da ilimi su shiga tsarin bada matsayi na ƙasa

Gwamnatin Tarayya ta umarci jami’o’i, kwalejojin fasaha da ilimi su shiga tsarin bada matsayi na ƙasa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin shiga cikin tsarin tantancewa da tsara matsayin manyan makarantun ilimi na ƙasa ya zama wajibi ga dukkan jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi da ke faɗin ƙasar. Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, yayin wata ganawa da Kwamitin Ba da Shawara kan Matsayin Jami’o’in Nijeriya, wanda aka faɗaca aikinsa tare da sauya masa suna zuwa Kwamitin Ba da Shawara kan Matsayin Manyan Makarantun Ilimi na Nijeriya. A cewar wata sanarwa da Ikharo Attah, Mai Ba Ministan Ilimi Shawara kan Yaɗa Labarai…
Read More
Karfin soji kaɗai ba zai kawo ƙarshen matsalar tsaro ba — Tinubu

Karfin soji kaɗai ba zai kawo ƙarshen matsalar tsaro ba — Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce amfani da ƙarfin soji kaɗai ba zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya ba, inda ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar gwamnati, jami’an tsaro da al’umma wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron tsaro na Arewa ta Tsakiya na shekarar 2026 da aka gudanar a Makurdi, Jihar Benue, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilce shi. Ya ce rashin tsaro ya zama matsala mai sarƙaƙiya da ba wata hukuma, wani matakin gwamnati ko wata…
Read More
An kori jami’an EFCC sama da 40 kan cin hanci — Olukoyede

An kori jami’an EFCC sama da 40 kan cin hanci — Olukoyede

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki ta ƙasa (EFCC) ta ce ta kori fiye da ma’aikatanta 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata, sakamakon zargin cin hanci da sauran laifukan da suka shafi kuɗi. Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana haka a Abuja yayin ganawarsa da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yan jarida. Ya ce fiye da biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari’a, yayin da ake shirya takardun wasu domin gurfanar da su gaban kotu. Olukoyede ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa jami’an…
Read More
An kama wata mata za ta kai wa ɗanta miyagun ƙwayoyi a gidan yari

An kama wata mata za ta kai wa ɗanta miyagun ƙwayoyi a gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) sun kama wata mata da ake zargi da ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyi cikin Gidan Gyaran Hali na Ibara da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, domin kai wa ɗanta da ke tsare a gidan. Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Ogun, Odukoya Olayinka, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce an kama matar mai suna Misis Iyabo Sowunmi ne yayin da jami’an tsaro ke gudanar da bincike a babbar ƙofar shiga gidan gyaran halin. Ya ce jami’an sun…
Read More
Ya zama dole a mutunta haƙƙin El-Rufai —Majalisar ƙoli ta Shari’a

Ya zama dole a mutunta haƙƙin El-Rufai —Majalisar ƙoli ta Shari’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar ƙoli ta Shari’a ta Nijeriya (SCSN) ta sake nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, tana mai cewa dole ne a mutunta haƙƙinsa tare da tabbatar da an bi ƙa’ida a shari’ar da ake yi masa. A wata sanarwa da Sakataren-Janar na majalisar, Nafiu Baba-Ahmad, ya fitar, SCSN ta ce El-Rufai, kamar kowane ɗan Nijeriya, ana ɗaukar sa marar laifi, har sai kotu ta tabbatar da laifinsa. Tsohon gwamnan na fuskantar shari’a kan zarge-zargen da suka haɗa da cin amanar ofis, zamba, bayar da kwangiloli ba…
Read More
Batagari sun soke mutane uku har lahira yayin zagayen Mauludi a Bauchi

Batagari sun soke mutane uku har lahira yayin zagayen Mauludi a Bauchi

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi An samu tashin hankali yayin zagayen bikin Mauludin Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a garin Bauchi da kewaye, inda wasu matasa uku suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren daba da wasu bata gari suka kai musu. An gudanar da zagayen Mauludin ne a ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, wanda ya yi daidai da 12 ga Rabi'ul Awwal, 1448 bayan Hijira. Taron ya samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na Jihar Bauchi da wasu jihohin Nijeriya. Duk da armashin da aka yi wa zagayen Mauludin, lamarin ya samu tangarɗa bayan da wasu bata gari…
Read More
ZASCOSA ta ƙaddamar da kwamitoci 10 gabanin babban taronta a Nuwamba

ZASCOSA ta ƙaddamar da kwamitoci 10 gabanin babban taronta a Nuwamba

Daga GAMBO ISA a Abuja Kungiyar ZASCOSA ta ƙasa ta ƙaddamar da ƙananan kwamitoci guda 10 domin jagorantar ayyukan ƙungiyar da kuma sauƙaƙa shirye-shiryen taronta na shekara-shekara (AGM) da kuma Bikin Dinner da Raba Kyaututtuka da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamban shekarar 2026. Shugaban ZASCOSA na ƙasa, Esɓ. Dung Nehemiah Rwang, ne ya ƙaddamar da kwamitocin a ranar Asabar. Rwang ya ce an zaɓi waɗanda za su jagoranci kwamitocin cikin tsanaki, bayan tuntuɓar shugabannin rassan ƙungiyar daban-daban ko wakilansu, bisa la’akari da ƙwarewa da gogewar da suke da ita a fannoni daban-daban. Ya ce kafa kwamitocin ya zama wajibi…
Read More
Wani Kirista ya gina masallacin Juma’a a Filato

Wani Kirista ya gina masallacin Juma’a a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani Kirista mazaunin Jihar Filato, Peter Ibrahim Gyendyeng, ya gina wa al’ummar Musulmi Masallacin Juma’a a yankin Gana Ropp da ke ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a jihar. Ginin masallacin ya faranta wa al’ummar Musulmin yankin rai, inda suka bayyana matakin a matsayin wata alama ta haɗin kai da kuma nuna cewa su ma suna da muhimmiyar rawa a cikin al’umma. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar Kiristoci da Musulmi a wasu sassan Jihar Filato ke fuskantar ƙalubale sakamakon rikice-rikicen da suka faru a yankin, musamman a ƙaramar Hukumar Barkin Ladi. Da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin samar wa ƙwararrun ’yan Nijeriya damar aiki a ƙasashen waje

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin samar wa ƙwararrun ’yan Nijeriya damar aiki a ƙasashen waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna “Hire from Nigeria”, domin bai wa ƙwararrun ’yan Nijeriya damar yi wa kamfanoni da masu ɗaukar ma’aikata na ƙasashen waje aiki daga cikin ƙasar. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishinsa da ke Abuja. Idris ya ce ƙaddamar da shirin wani muhimmin mataki ne na sanya ɗaya daga cikin manyan kadarorin Nijeriya, wato ɗimbin al’ummarta masu ƙwarewa, a sahun gaba wajen hulɗar tattalin arzikin ƙasar…
Read More
Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya ziyarci rundunar ’yan sandan Kano gabanin zaɓen 2027

Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya ziyarci rundunar ’yan sandan Kano gabanin zaɓen 2027

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta karɓi baƙuncin wata tawaga daga Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa (National Peace Committee), ta hannun Sakatariyar Cibiyar Kukah, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Tawagar ta ziyarci rundunar ne a ranar Talata, 1 ga Satumbar 2026, ƙarƙashin jagorancin Mista Espom Ajanya, ƙaramin Manajan Shirye-shirye na Cibiyar Kukah, wadda ke aiki a matsayin Sakatariyar Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa. Da yake jawabi yayin ziyarar, Ajanya ya ce tattaunawar na daga cikin shirye-shiryen Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa gabanin babban zaɓen…
Read More