06
Sep
Daga MUHAMMADU MUJITABA a KANO Kungiyar Ma’aikatan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (ASUSS), ƙarƙashin jagorancin Kwamared Abdu Usman Yalo, ta yaba wa hukumar Makarantar ’Yan Mata ta Mairo Tijjani Government Science and Technical College Kano (MTGSCK), ƙarƙashin shugabancin Hajiya Rabi Jafar Baba, kan yadda ta shirya taron karrama ɗalibai, malamai da shugabannin makarantu da suka nuna ƙwazo da bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa ilimi da sauran fannoni na rayuwar al’umma. An bayyana hakan ne yayin wani taron raba kyaututtuka da makarantar MTGSCK ta shirya a Kano a makon da ya gabata. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ASUSS…
