ukarofi

12479 Posts
Shaye-shaye da illolinsu ga matasa, lafiya da zamantakewa

Shaye-shaye da illolinsu ga matasa, lafiya da zamantakewa

Daga BILKISU YUSUF ALI PhD Shaye-shaye na cikin manyan matsalolin da ke addabar al'ummomi a duniya, musamman matasa. Matsalar tana shafar lafiyar jiki da ta kwakwalwa da ilimi da tattalin arziki da tsaro da zamantakewar al'umma. Wannan rubutu ta yi  nazari kan ma'anar shaye-shaye da nau'o'insu, abubuwan da ke jawo matasa shiga shaye-shaye, illolinsu ga lafiyar mutum da zamantakewa, tare da hanyoyin kariya da magance matsalar. Bincike ya nuna cewa haɗin gwiwar iyaye da malamai da shugabannin addini, gwamnati da al'umma yana da muhimmanci wajen rage wannan matsala. Gabatarwa Matasa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al'umma. Idan aka ba su…
Read More
Masu gine-gine sun yi gargaɗin tsadar siminti na ƙara tsananta matsalar gidaje

Masu gine-gine sun yi gargaɗin tsadar siminti na ƙara tsananta matsalar gidaje

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Masu harkar gine-ginen gidaje a Nijeriya sun yi gargaɗin cewa tashin farashin siminti na ƙara tsananta matsalar rashin gidaje mai sauƙin haya ko saya a ƙasar, yayin da Hukumar Kula da Gasa da Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC) ke gudanar da bincike kan yadda ake ƙayyade farashin siminti. Binciken kasuwa ya nuna cewa farashin buhun siminti mai nauyin kilogiram 50, wanda ake sayarwa tsakanin N9,300 zuwa N9,700 a watan Janairun 2026, ya haura zuwa kusan N15,000 a wasu wurare zuwa watan Yulin bana. Wannan ƙarin farashi na zuwa ne a daidai lokacin da masu…
Read More
Bankuna ne suka kai kashi 92 na rahoton haramtaccen hada-hadar kuɗi a 2025 — NFIU

Bankuna ne suka kai kashi 92 na rahoton haramtaccen hada-hadar kuɗi a 2025 — NFIU

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bankunan ajiyar kuɗi na Nijeriya sun gabatar da kusan kashi 92 cikin 100 na rahotannin hada-hadar kuɗi da ake zargi da aikata laifi da Hukumar Leƙen Asirin Kuɗi ta Nijeriya (NFIU) ta karɓa a shekarar 2025, duk da cewa adadin irin waɗannan rahotanni ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarar 2024. Hakan na ƙunshe cikin rahoton shekara-shekara na NFIU na 2025, wanda ya nuna cewa hukumomi da cibiyoyin da doka ta wajabta musu kai rahoton hada-hadar kuɗi sun gabatar da rahotannin Hada-hadar Kuɗaɗe Da Ake Zargi (STR) guda 42,082 a cikin shekarar. Daga cikin wannan…
Read More
NUPRC ta ba kamfanonin rijiyoyin mai 31 kwanaki 60 su biya haƙƙoƙi

NUPRC ta ba kamfanonin rijiyoyin mai 31 kwanaki 60 su biya haƙƙoƙi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta bai wa kamfanoni 31 da suka yi nasarar lashe rijiyoyin mai da iskar gas 37 a zagayen bayar da lasisin haƙar mai na shekarar 2025 wa’adin kusan kwanaki 60 domin biyan kuɗaɗen da ake buƙata, ko su yi asarar lasisin da aka ba su na wucin gadi. Gargaɗin ya zo ne wata guda bayan gudanar da taron tantancewa da bayar da lasisin kasuwanci da aka yi a Abuja ranar 21 ga Yuli, 2026, inda aka sanar da sunayen kamfanonin da suka yi nasara a gasar neman…
Read More
NNPC da abokan hulɗarsa sun sa hannu kan yarjejeniyoyin aikin Bonga Southwest na Dala biliyan 21

NNPC da abokan hulɗarsa sun sa hannu kan yarjejeniyoyin aikin Bonga Southwest na Dala biliyan 21

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) da abokan hulɗarsa a kan Yarjejeniyar Haƙar Mai ta OML 118 sun rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyin kasuwanci da suka shafi aikin haƙar mai da iskar gas na Bonga Southwest/Aparo da ke zurfin teku. Ana sa ran matakin zai hanzarta aikin zuwa matakin ƙudurin zuba jari na ƙarshe, wato Final Inɓestment Decision (FID), tare da buɗe ƙofar zuba jarin da zai iya kaiwa tsakanin dala biliyan 15 zuwa 21. Babban Daraktan Rukunin NNPC Limited, Bayo Ojulari, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce kamfanin tare da Shell…
Read More
Sojoji sun halaka kwamandoji biyu na ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Maha a Katsina

Sojoji sun halaka kwamandoji biyu na ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Maha a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun halaka manyan kwamandoji biyu na wata ƙungiyar ‘yan ta’adda ƙarqashin jagorancin ƙasurgumin ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu Filani, a ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina. Rundunar ta ce an halaka mutanen biyu, Hamisu, wanda aka fi sani da Mamiyo, da Umar Bocho, ne a wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a kusa da ƙauyen Kogo ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026. Jami’in yaɗa Labarai na Operation FANSAN YAMMA, Lt. Col. Aliyu Danja, ya ce dakarun Sector 2 sun yi arangama da ‘yan…
Read More
Yadda aka gabatar da taron littafin waƙoƙin tambarin zamani a Kano na matashiya Salma Mailambu

Yadda aka gabatar da taron littafin waƙoƙin tambarin zamani a Kano na matashiya Salma Mailambu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An gabatar da sabon littafin wakokin tambarin zamani, wanda matashiyar mawaƙiya Salma Saeed Mailambu ta rubuta, a wani babban taro da aka gudanar a ɗakin taro na Gidan Mambayya da ke Unguwar Gwammaja, a cikin birnin Kano, inda manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta. Taron ya samu halartar malamai, ɗalibai, masana da masu nazarin waƙoƙin Hausa da al’adun gargajiya, waɗanda suka taru domin taya mawaƙiyar murnar wannan gagarumar nasara tare da ƙarfafa mata gwiwa wajen ci gaba da ayyukan adabi. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin shirya ƙaddamar da littafin,…
Read More
’Yan bindiga sun kashe shugaban APC na Rantan tare da jikkata wasu biyar a Kano

’Yan bindiga sun kashe shugaban APC na Rantan tare da jikkata wasu biyar a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano ’Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe Alhaji Garba Buba, shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Rantan da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Jihar Kano. Rahotanni sun ce maharan sun shiga garin Rantan ne a daren Lahadi, inda suka buɗe wa jama’ar garin wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani mazaunin garin mai suna Sulaiman Zunduma. Wani mazaunin garin, Hamza Isah Rantan, ne ya tabbatar da faruwar harin a wani saƙo da ya wallafa a Facebook, inda ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Ya ce…
Read More
Dakta Margaret Elayo ta miƙa mulki ga Hon. Rebecca Adamu Kpadji

Dakta Margaret Elayo ta miƙa mulki ga Hon. Rebecca Adamu Kpadji

Daga JOHN WADA a Lafiya Kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta jihar Nasarawa gimbiya Dr. Margaret Elayo ta miƙa ragamar jagorancin ma’aikatar harkokin mata da cigaban jama’a ga sabuwar kwamishiniya Hon. Rebecca Adamu Kpadji. An gudanar da bikin miƙa mulkin ne a sakatariyar gwamnatin jihar dake Lafiya. Wannan ya kuma nuna farawar sabon jagoranci a cikin ma’aikatar. A lokacin bikin Dr. Margaret Elayo ta roƙi ma’aikata da shugabannin ma’aikatar da su ba sabuwar kwamishiniyar cikakken goyon bayan da suka ba ta. Ta jaddada cewa Hon. Kpadji ba baƙuwa ba ce a ma’aikatar harkokin matan domin ta yi ritaya daga…
Read More
Zuwa gare ku ma’abota haƙuri

Zuwa gare ku ma’abota haƙuri

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Zuwa gare ku, ya ma’abota haƙuri, ku da kuka zaɓi ku tsaya daram a kan gaskiya duk da tsanani, ku da kuka rungumi haƙuri a lokacin jarrabawa, ku da kuka yi imani cewa duk wani raɗaɗi da zubar hawaye ba zai tafi a banza ba a wajen Allah Maɗaukaki. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne domin girmama ku, domin tunatar da ku darajar haƙuri a Musulunci, da kuma ƙarfafa zuciyarku da kalaman Alƙur’ani da hadisai, waɗanda suka nuna cewa haƙuri ita ce hanya zuwa ga nasara ta gaskiya. Haƙuri ba kawai jurewa ba ne.…
Read More