01
Sep
Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Wannan matsala, kamar sauran duk matsaloli da ke kawo cece-kuce a musulunci ba sabuwar matsala ba ce, domin ta faro akalla tun lokacin tabi’ai. Kamar sauran matsaloli za ka samu cewa akasari watsi da cikakkiyar koyarwa ta Qur’ani ke kawo su. Musulunci ya fara samun matsaloli tun bayan rasuwar annabi, sakamakon rarrabuwar kawuna da siyasa ta bijiro da su sakamakon halifanci, kuma wannan banbanci sannu a hankali sai ya tashi daga siyasa ya koma akida, abinda ya haifar da akidojin shi’anci, Kharijawa da Yan sunna da sauransu. Hakan ya haifar da kirkire-kirkire na hadisai wajen kokarin…
