Ba a yarinta kuma ba a tsufa a siyasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wasu rahotanni da suka mamaye kafofin watsa labarai a cikin makon jiya, na bayyana cewa jagoran Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas mai neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa na 2023 wato Ahmad Bola Tinubu ya bayyana a fadar Sarkin Yarabawa, Alaafin na Oyo, cewa matasan Nijeriya da ke ƙorafin tsofaffin ’yan siyasa sun mamaye harkar mulki a Nijeriya, su yi haƙuri ba yanzu za su samu mulkin ƙasar nan ba, sai bayan ya yi nasa mulkin.

Tinubu mai shekaru 69 na daga cikin ’yan siyasar da suka daɗe suna ƙulafacin sai sun mulki ƙasar nan, yana ganin lokacin da za a sake wa matasa ragamar tafiyar da harkokin mulki a ƙasar nan bai kai ba. Duk kuwa da wani umurni da aka ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar a wata majiya cewa, a riƙa la’akari da matasa wajen rabon muƙamai da shugabancin riƙon ma’aikatu da hukumomi ko wasu muhimman kwamitoci, domin shirya su ga babban nauyin shugabanci a nan gaba.

Sannan da kuma sanya dokar da shugaban ƙasar ya yi kan dokar da ta bai wa matasa damar shiga fagen neman muƙaman siyasa a shekarar 2018, dokar da aka fi sani da ‘Not Too Young To Run Bill’.

Waɗannan kalamai na Tinubu ba su yi wa wasu matasa da ke da ra’ayin siyasa daɗi ba, inda har ya jawo muhawara mai zafi a zaurukan sada zumunta daban-daban, kan buƙatar sake wa matasa mara su shiga gwamnati a dama da su a sha’anin mulki da jagoranci. Ko da yake wasu na ganin lallai akwai sauran lokaci ga matasan Nijeriya, saboda rashin ƙwarewa, zarmewar zuciya da tsoron faɗawa cikin almubazzaranci da satar dukiyar ƙasa, da kuma uwa rabuwar kan matasa kan bambancin addini da ɓangaranci. 

Wannan shi yake ƙarfafa gwiwar wasu tsofaffin ’yan siyasar da marasa kishin cigaban matasa da ke ganin riƙon shugabancin ƙasa ko Gwamna ba na matasa ba ne, gara dai a ja su a jiki don amfani da ilimin su da ƙuruciyarsu wajen yaƙin neman zaɓe da tayar da ƙayar baya a inda ɗan siyasa ke ganin za a tauye masa wata dama ta cimma burin sa. Duk kuwa da ƙorafe ƙorafen da matasa daga ɓangarori daban-daban na ƙasar nan ke yi na cewa sun gaji da riƙewa tsofaffin ’yan siyasa ƙaho suna ta tatsar nono su manta da su, sai dai ’ya’yan su.

Ita wannan doka da ta bai wa matasa damar shiga fagen neman muƙaman siyasa, wacce kuma ta samu amincewar Majalisar Ƙasa ta rage yawan shekarun da ake buƙata ga mai neman takarar shugaban ƙasa daga shekara 40 zuwa 30. Ga mai son takarar Gwamna kuma daga shekara 35 zuwa 30. Mai neman takarar kujerar ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya kuwa nan ma an rage shekarun daga 30 zuwa 25. Haka ma adadin shekarun yake ga mai neman takarar kujerar ɗan Majalisar Dokoki ta Jiha.

An yi haka ne, a cewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari don a bai wa matasa masu kishi da burin shiga sahun masu mulki a Nijeriya damar bayyana buƙatar su da kuma neman yardar ’yan ƙasa game da muƙamin da suke nema.

Daga cikin koke-koken masu zanga zangar neman samar da sauyi a harkokin tafiyar da ƙasa da akasari matasa ne suka jagorance ta, wato lokacin EndSars, akwai batun bai wa matasa dama cikin harkokin mulki da shugabanci, domin kawo sabbin tunani da tsare-tsare da suka dace da zamani, da nufin kawo sabon canji a rayuwar ’yan Nijeriya.

Kenan za mu fahimci cewa, matasan ƙasar nan sun jima suna bayyana buƙatar su ta neman a ba su dama, su ma su ba da tasu gudunmawar a harkokin mulki da siyasa, ba sai a matsayin ƙananan ma’aikata, jami’an tsaro ko ’yan bangar siyasa ba.

Duk kuwa da wannan doka ta ‘Not Too Young To Run’ da aka kafa ƙalilan ne daga cikin matasan suka samu zarafin fitowa su nuna buƙatar su ta neman takara, saboda ƙalubalen da tun dama suke kuka a kan su cewa, suna musu tarnaƙi ga shiga siyasa suna nan ba a kawar da su ba. Kamar dai batun rashin kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, siyasar ubangida, tsadar takardun neman shiga takara ƙarƙashin jam’iyyu, da babakeren manyan ’yan siyasa, suna hana matasa fitowa da ƙarfin su a dama da su a harkokin siyasa, duk kuwa da kasancewar doka ta ba su wannan damar.

Tsarin tafiyar da siyasar Nijeriya, wanda aka ce ana kwaikwayon siyasar Amurka ne, ba ya koyi da salon Amurkawa yadda muke iƙirari. Domin kuwa idan muka yi nazarin irin yadda Amurkawa ke zaɓar shugabannin su za mu fahimci cewa, gogewa da salon yaƙin neman zaɓenka, da yadda ka shirya tunkarar kawo wa al’ummar ƙasar sauyi daga matsalolin da suke fuskanta shi ne abin da ya fi bai wa ɗan takara tagomashi, komai tsufansa ko ƙuruciyarsa.

Kamar misali, a shekarar 1960 Amurkawa sun zaɓi John F. Kennedy mai shekaru 42 a matsayin shugaban ƙasa, amma sai ga shi a shekarar 1980 sun zavi dattijo Ronald Reagan mai shekaru 70, bayan sa kuma an zo an zaɓi Bill Clinton mai shekaru 46 a shekarar 1992. 

Haka kuma su Amurkawan ne dai suka zavi Barack Obama mai shekaru 47 a shekarar 2008, amma a bayan sa kuma suka zaɓi Donald Trump ɗan shekara 70. Ga kuma mataimakin sa da ya gaje shi Joe Biden mai shekaru 79. 

Bai kamata shekaru su zama mizani na zaven ɗan takara ba, matuƙar yana da gogewa da ilimin da zai taimaka masa wajen jagorancin al’ummarsa. Tun da muna ganin yadda masu ƙananan shekaru ke mulki a wasu ƙasashen, kuma suke samar wa ƙasashen nasu cigaba. 

Ba da jimawa sosai ba, mun ga yadda al’ummar a shekarar 2017 ƙasar Faransa suka zaɓi shugaba Emmanuel Macron ɗan shekara 39, a maimakon abokiyar adawarsa Marine Le Pen mai shekaru 53. 

Ya kamata a ce siyasar Nijeriya ta yi riƙar da za ta daina kallon shekaru a matsayin wani shinge na hana wani rukunin mutane, ko don saboda shekarun su ko jinsin su, ko yankin da suka fito damar shiga takara ko neman wani muƙamin siyasa a gwamnati. Kowa da irin baiwar sa da kuma irin gudunmawar da zai iya bayar wa ga ci gaban ƙasa. 

A ƙarshen makon da ya gabata ma mun ga wata dattijuwa mai shekaru 102 da ake kira Nonye Josephine Ezeanyaeche daga Jihar Anambra ta bayyana ta kafar talabijin a babban talabijin na ƙasa NTA, inda ta bayyana aniyarta na shiga takarar shugabancin ƙasar nan a 2023, saboda a cewar ta ba a tsufa a siyasa, don haka tana neman goyon bayan ‘yan Nijeriya kan takarar da za ta yi. 

Ko da yake bai saɓa wa dokar ƙasa ba, ire-iren su Bola Ahmad Tinubu mai shekaru 69 da tsohuwa Nonye Josephine Ezeanyaeche su shiga neman takara ba, matuƙar suna da cikakkiyar lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa, da za su iya tunkarar matsalolin ƙasa da kawo dabarun warware su. Kuma matuƙar za a saurari wannan tsohuwa da shekarun ta suka doshi gargarar Kabari Salamu Alaikum, wajen neman shugabanci to, matasa ne suka fi dacewa da wannan damar. 

A wani rubutu da ya yi a shafukansa na zaurukan sada zumunta wani matashin ɗan siyasa mai kishin kawo sauyi a rayuwar matasa a siyasar ƙasar nan daga Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai mai laƙabi da Ɗawisu, wanda kuma jigo a tafiyar wata sabuwar ƙungiya ta We2Geda, bayan wani taron gangamin kafa ƙungiyar haɗin kan ‘yan siyasa masu burin karɓar gwamnati a babban zaɓen 2023 ta The National Movement (TNM), wanda ya gudana a Abuja, ya shawarci manyan ‘yan siyasa kan tafiya da matasa. 

Ya ce, ‘Ni shawara ta ga iyayen namu na TNM (kai har ma da manyan jam’iyyun mu na APC da PDP) shi ne, su zamo fitilar haska wa matasa gabas wajen ganin mun ɗau hanyar kawo sauyi akan salon mulki da ake gabatar wa a ƙasar nan. Su taya mu nemo matasa masu zafi a jika, masu nagarta da inganci, waɗanda su kai fice a ƙananan shekaru wajen hidimar al’umma ko kuma ma’aikatan da suka nuna hazaƙa da ƙwarewa a shekaru ƙalilan. Tabbas akwai su bila’adadin a ƙasar nan, kuma irin su ya kamata ƙungiyar TNM su saka a gaba a matsayin su na iyaye. Kai hasali ma a shirye muke mu ba su gurbi na Kwamitin Dattijai a cikin tafiyar mu ta We2Geda dan ganin an samu nasara.’

Lallai wannan tunani na Ɗawisu ya yi daidai da manufar rubutun mu na wannan mako, inda muke so a farkar da zukatan matasa da ‘yan siyasa, su sake yi wa fasalin siyasar ƙasar nan gyaran fuska, domin kawo sabbin sauye sauye da za su ɗora ƙasar nan kan turba tagari. 

Sannan kamar yadda wani matashin ɗan siyasa kuma shugaban Majalisar Shiga Tsakanin Jam’iyyun Siyasa ta IPAC a Jihar Filato, Abubakar Dogara ya ke faɗa a wata zantawa da muka yi ya buƙaci gwamnatin tarayya ta dawo da tsarin ɗaukar nauyin jam’iyyun siyasa masu rijista da ba su tallafin gudanar da harkokin siyasar Jam’iyya da fitar da ‘yan takara, domin ƙananan jam’iyyu da ba su da gwamnati su samu ƙwarin gwiwar tafiyar da harkokinsu. Kuma wannan zai bai wa matasa damar mallakar takardun shaidar tsayawa takara cikin rahusa. 

Har wa yau, kamar yadda ake bai wa mata tallafi don ƙarfafa musu gwiwar shiga takara, ya kamata su ma matasa a ba su irin wannan goyon bayan, ta hanyar ba su takardun neman tsayawa takara kyauta ko cikin rangwame da kuma ware musu adadin wasu kujeru da za a ce sai matasa da shekarun su ba su haura 35 ba ko misalin haka, don ba da damar da wasu masu rabo daga cikin matasa za su samu damar shiga a dama da su.