Nijeriya ta yi zargin jami’an tsaron Ukraine na hana ‘yan Nijeriya ficewa daga ƙasar zuwa Poland

Daga BASHIR ISAH

Yayin da ake shirin tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Ukraine, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ‘yan Nijeriya kimanin mutum dubu huɗu haɗe da wasu ‘yan Afrika da dama ne suka maƙale a Ukraine.

Sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu a ranar 27 ga Fabrairu ta ce, “Abu ne mai daɗaɗɗen tarihi yadda ‘yan Nijeriya da sauran ‘yan Africa ke tafiya karatu a ƙasar Ukraine, musmaman ma don nazarin likitanci. Kuma galibin ɗaliban ‘yan jami’a ne.”

Garba Shehu ya ci gaba da cewa wani sahihin hoton bidiyon da gwmanati ta samu ya nuna yadda ‘yan sanda da jami’an tsaron Ukraine suka muzanta wa ‘yan Nijeriya shiga motoci da jirgin ƙasar da ke jigilar mutane zuwa kan iyakar Ukraine da Poland.

Haka nan, ya ce akwai rahoto kan yadda jami’an Poland suka hana ‘yan Nijeriyar da suka fito daga Ukraine shiga ƙasarsu.

A cewar Garba Shehu, “Wata ƙungiyar ɗaliban Nijeriya da aka hana su shiga Poland sun yanke shawarar komawa ta Ukraine don su samu ficewa daga ƙasar ta iyakar Hungary.

“Muna sane da irin wahala da kuma tsoron da waɗanda suka tsinci kansu cikin wannan hali suke fuskanta.”

Sanarwar ta nuna cewar ita ma Nijeriya ba za a bar ta baya wajen bada gudunmawarta ta hanyar da ta sawaƙa wajen kawo ƙarshen yaƙin da ya ɓalle tsakanin Ukraine da Rasha.