Cikakken rahoto: Faruk Lawan bai nemi cin hanci daga Otedola ba, inji Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙarar, wacce ta ke zamanta a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, ta tabbatar da cewa, masu gabatar da ƙara ba su iya tabbatar wa kotu da cewa, tsohon fitaccen ɗan Majalaisar Wakilai ta Nijeriya, Hon. Faruk Lawan, ya nemi attajirin nan, Mista Femi Otedola, ya ba shi cin hancin Dala Miliyan Uku, don ya zare sunan kamfaninsa, Zenon Oil and Gas Limited, daga jerin kamfanonin da suka damfari Nijeriya kan kuɗin tallafin mai ba a cikin rahoton Kwamitin Musamman na majalisar, wanda Hon. Lawan din ya jagoranta a 2012.

Wannan dalili ya sanya Kotun Ɗaukaka Ƙarar yin fatali da zarge-zarge guda biyu (na farko da na biyu) da masu gabatar da ƙarar suka yi, inda kuma hakan ta rage hukuncin daga shekara bakwai zuwa biyar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin hukuncin da kotun ta yanke a ranar Alhamis, 24 ga Fabrairu, 2022, ƙarƙashin jagorancin Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Nijeriya, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, tare da wasu alƙalan guda biyu, inda suka suka yi fatali da hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yanke a cikin watan Yuni, 2021, lokacin da aka yanke wa tsohon ɗan majalisar hukuncin zaman gidan jarun na shekara bakwai.

Sai dai kuma alƙalan sun amince da zargin na uku da aka yi wa Faruk Lawan, saboda iƙirarin da ya yi da bakinsa na amsar kuɗin, duk da ya yi togaciyar cewa, ya karɓa ne, don ya sanar da jami’an tsaro cewa, Mista Otedola ya ba shi cin hanci na Dala 500,000 a yayin da kwamitinsa ke bincike kan badaƙalar tallafin man fetur. Don haka sai alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙarar suka ce, sun amince da hukuncin Babbar Kotu kan zargi na uku, wanda aka yanke masa hukuncin shekara biyar gidan kaso.

A yayin da alƙalan guda uku ke zaman yanke hukuncin sun ce, sun dogara da gazawar masu bincike ne kafin yanke hukuncin, domin ba su iya kawo wata ƙwaƙƙwarar shaida da ta nuna cewa, Lawan ne ya nemi a ba shi cin hanci ko kuma Otedola ne ya nemi ya ba shi ba, don a cire sunan kamfaninsa daga zargi.

Alƙalan sun ƙara da cewa, dan sandan da ya gudanar da bincike kan lamarin a matsayin shaidar masu tuhuma na biyu, David Igbodo, “ya yi ta zilliya, kauce-kauce ko noke-noke” a gaban kotu kan hira a waya da mutanen biyu suka yi kan batun karɓar rashawar. Alƙali Dongban-Mensem ta ce, ya kamata masu gabatar da ƙara su nemi cikakkun bayanan tattaunawar dukkan mutanen biyu, amma suka gaza yin hakan.

“Masu gurfanar da wanda ake zargi ba su yi la’akari da cewa dole ne su tuntubi kamfanonin sadarwa, don tabbatar da tabbacin ko wanda ake zargin din ya nemi cin hancin Dala Miliyan Uku daga shaidar masu kara na biyar ba (wato Otedola),” inji alƙalin, wacce ta kara da cewa, iƙirarin na Otedola, wanda ya ce, Lawan ne ya nemi ya ba shi cin hanci, bai kawo wata hujja da za a iya dogara da ita ba.

A ta bakin alƙalin, “babu wata tartibiyar shaida, wacce shaida na biyu (Mista Igbodo) ya tabbatar ko ya bayar cewa wanda ya ɗaukaka ƙarar (Lawan) ya nemi shaida na biyar (Mista Otedola) ya ba shi cin hanci. Babu kuma wata shaida da ta nuna cewa, mai ɗaukaka ƙarar (Lawan) ya amince ya karbi Dala Miliyan Uku daga shida na biyar (Otedola), don ya cire kamfanonin Zenon Oil and Gas Limited da AP Petroleum daga jerin sunayen kamfanonin da rahoto ya kama da laifi.”

A yayin da alƙalin ke watsi da zarge-zargen gida biyu, ta yanke hukuncin cewa, “akwai babban gibi a zargi na 1 da na 2. Babu tartibiyar hujja kan mai ɗaukaka ƙara a zargi na 1 da na 2.”

Amma yayin da alƙalin ke tabbatar da hukunci kan laifi na biyu da ƙaramar kotun ta yanke na cewa, Faruk Lawan ya amshi Dala 500,000 daga Otedola har aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyar, Mai Sharia Dongban-Mensem ta ce, iƙirarin Lawan na cewa, ya amshi kuɗin ne, ya samu hujjar Otedola ya nemi ya ba shi cin hanci, ba gaskiya ba ne, tana mai cewa, a lokacin gudanar da shari’ar babu inda wani bayani ya nuna cewa, Lawan ya sanar da wata hukumar tsaro kuɗin da Otedola ya ba shi.

“Abin dubawa ne yadda ya amshi Dala 500,000 a matsayin shaidar an ba shi cin hanci, amma ya kasa miƙa su ga kowacce hukumar tsaro,” inji ta, tana mai kafa hujja da wani dan majalisar da suka yi aiki tare da Lawan mai suna Hon. Adams Jagaba, wanda ya zo gaban kotun a matsayin shaidar masu gabatar da kara na huɗu, inda ya ƙaryata Faruk Lawan bisa iƙirarin da na ya mika kudin tare da wasikar sanarwa. “Babu kuɗi ko takardar da aka bai wa shaida na hudu,” inji alƙalin.

A yayin da kotun ke tabbatar da zargin na uku da kuma hukuncin kotun baya, sai alƙalin ta ce, masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin “ba tare da kokwanto ba,” tana mai tabbatar da laifin da kuma hukuncin na shekara biyar, amma nan take ta rushe hukuncin zargi na 1 da 2 na shekara bakwai.

Asalin badaƙalar:
Hon. Faruk Lawan, wanda yana cikin ’yan Majalisar Wakilai, waɗanda aka buɗe majalisar da su a 1999 lokacin da Nijeriya ta dawo mulkin farar hula, ya shugabanci Kwamitin Musamman da ya binciki badaƙalar wawure kudin tallafin mai a ƙarƙashin tsohuwar Gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan a 2012.

A lokacin a na yi wa Faruk Lawan laƙabi da ‘Mr. Integrity’, wato ‘Mai Nagarta’, saboda fafutukar da ya ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa a majalisa, musamman ma a lokacin da ya jagoranci wata ƙungiyar ’yan majalisa mai suna ‘Integrity Group’.

A ƙarshen binciken da kwamitin nasa ya gabatar, ya miƙa rahoton da ya kama wasu kamfanoni da yin kwana da aƙalla Naira Tiriliyan 2.6, ciki har da kamfanin Otedola mai suna Zenon Oil and Gas. Kwamitin ya kama kamfanin Zenon da laifin amsar Dala Miliyan 230 daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), don shigo da fetur Nijeriya, amma ya gaza yin hakan.

Sai dai kuma daga bisani an zargi Lawan da cire sunan Kamfanin Zenon daga jerin sunayen bayan da ya amshi Dala 500,000 daga Mista Otedola a matsayin kason farko na cin hancin Dala Miliyan Uku da suka yi ‘yarjejeniya’, kamar yadda aka sanar da alƙalin.

Sai dai kuma daga bisani dukkan mutanen biyu sun yi iƙirarin cewa, sun amsa ko miƙa kuɗin ne a matsayin shaida kan junansu kawai. Amma shi Otedola ya yi iƙirarin ya mika rahoton hakan ga Hukumar ’Yan Sandan Farin Kaya (SSS). Attajirin ta ƙara da cewa, Hukumar SSS ta nemi ya cigaba da biye wa Lawan din, sannan hukumar ta shirya dabarar yi wa Lawan lobe ta hanyar sanya kyamara a lokacin da zai ya amshi kuɗin cin hancin. A nasa ɓangaren, Faruk Lawan ya jaddada cewa, ya amshi kuɗin ne, don ya kafa hujja akan Otedola, amma bai iya samun damar kai rahoto ga kowacce hukumar tsaro ba.

Daga nan sai Ofishin Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a ta hannun babban lauya mai zaman kansa, Adegboyega Awomolo (SAN), ya gurfanar da Lawan a gaban Babbar Kotun Tarayya kan zargi na 1 da 2 a karkashin Sashe na 18(1)(a) da zargi na 3 a karkashin Sashe na 17(1)(a) na Kundin Dokar Cin Hanci da Rashawa da Dangoginsu na shekara ta 2000.

A ranar 22 ga Yuni, 2021, Alkalin Babbar Kotun Abuja, Mai Shari’a Angela Otaluka, ta yanke wa Faruk hukuncin bisa kama shi da dukkan laifukan da ake tuhumar sa da su. Kotun ta amince da dukkan zargin guda uku na neman a ba shi cin hancin Dala Miliyan Uku, amincewa ya amshi rashawar Dala Miliyan Uku da kuma amsar Dala 500,000 a matsayin cin hanci.

Sai alƙalin ta yanke wa Faruk hukuncin daurin shekara bakwai kan kowane laifi na 1 da na 2, sannan ya yanke masa hukuncin shekara biyar kan laifi na 3, amma zaman ɗaurin zai tafi a lokaci guda ne. Don haka shekara bakwai kenan zai yi, maimakon 19.

A na yanke wannan hukuncin ne sai Faruk Lawan ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara bisa rashin gamsuwa da hukuncin. Ya ɗauki hayar Babban Lauya Mike Ozekhome (SAN), a lokacin shari’ar ne, sannan kuma sai ya ɗauki hayar tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), Joseph Daudu (SAN), don ya tsaya masa a lokacin ɗaukaka ƙarar. Mista Daudu ya tono abubuwa shida a shari’ar ne. Ita kuwa Gwamnatin Tarayya ta samu wakilcin lauyan gwamnati, Aminu Halilu, ne, wanda ya soki dukkan hujjojin da mai ɗaukaka ƙarar ya yi.

A yayin yanke hukuncin ranar Alhamis da ta gabata, 24 ga Fabrairu, 2022, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta amince da hujja guda daga cikin shida da lauyan Faruk ya kawo, to amma wannan hujja guda ɗaya kacal ta isa ta sanya a wanke shi daga zargin aikata laifuka na 1 da na 2, wato neman a ba shi cin hanci da kuma da amincewa da hakan.

Kotun ta yi watsi da sauran hujjojin guda biyar, waɗanda za su iya kai wa ga soke dukkan tuhume-tuhumen bakiɗaya. Misali; an tuhumi Lawan ne a ƙarƙashin tsohuwar dokar ne ta 2000 maimakon wacce aka ƙirƙira a 2003. Amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta dogara da wani hukuncin Kotun Koli, wanda ya soke sabuwar dokar ta 2003, wanda hakan ke nuni da cewa ta 2000 ce halastaccoyar dokar wajen dogaro da hukuncinta. “Wallafa doka ba ya nufi halasci,” inji kotun.

Misis Dongban-Mensem ta ƙara da cewa, ko da an kuskure wajen dokar da aka tuhumi Lawan da ita, ba za a yi watsi da tuhumar ba matuƙar halastacciyar doka ta kama shi da laifin.

Lauyan ya kuma yi iƙirarin cewa, a matsayin Faruk Lawan na dan majalisa, yana da kariyar Dokokin Majalisar Wakilai, waɗanda da su ne ya kamata a tuhume shi, amma ba da dokar cin hanci da rashawa ba. A nan ma Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yi togaciya da cewa, babu wata doka da ta haramta a tuhumi dan Majalisar Wakilai da wata doka sai ta Dokokin Aikin Majalisar Wakilai kawai ba.

Lauyan ya kuma yi ƙorafin cewa, dan majalisar ba ma’aikacin gwamnati ba ne. Don haka bai cancanci a tuhume shi da dokar ma’aikata ba. Kotun ta ki yarda da wannan hujjar ma, tana mai cewa, tunda Lawan yana amsar albashi daga lalitar gwamnati, to tamkar ma’aikacin gwamnati ya ke.

Lauyan ya kuma kawo jayayyar cewa, akwai baki-biyu tsakanin Mista Otedola da wani ma’aikacin Majalisar Wakilai, Mista Boniface Emenalo, wanda ya zo a matsayin shaida 1 na masu gabatar da ƙara kan adadin kuɗin da Lawan ya amsa. Sai dai kotun ba ta yarda da wannan hujja a matsayin wacce za ta sa a kori tuhumomin ba, domin wanda ake tuhuma ya riga ya amince da ya amshi kuɗin da suka kai Dala 500,000.
Yanzu dai an zura idanu a ga mataki na gaba, wanda bai wuce zuwa Kotun Ƙoli ba, inda a can ne za a iya yanke hukuncin ƙarshe.

Shi dai Faruk Lawan a na kallon sa a matsayin dan majalisar da ya matsa wa Gwamnatin Jonathan zani da tsanani a wancan lokaci, inda gwamnatin ita kuma ta shirya masa gadar zare ta hannun Otedola ya rufta ciki.