Ba a yi wa Tinubu katangar hana shi ganin mutane ba, APC ta yi wa Ndume martani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC ta yi abin da Bahaushe ke cewa ‘ka fi mai kora sosawa’, yayin da ta nuna jin ciwon zafafan kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

APC ta yi masa raddin cewa kasa samun damar ganawar da Ndume ya yi da Tinubu ba zai taɓa zama dalili ko hujjar cewa wasu sun kange shugaban ƙasar daga ganawa da ‘yan Nijeriya ba.

Sakataren Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Feliɗ Morka ne ya yi wa Ndume wannan raddi, wanda ke ƙunshe cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar, a Abuja.

A cikin makon ne Sanata Ndume ya yi ƙorafin cewa “wasu ‘yan ba-ni-na-iya sun kange Tinubu daga ganin jama’a.

Ndume wanda ya ce ɓamɓare ƙananan hukumomi daga jikin gwamnonin jihohi ta hanyar samar masu ‘yancin cin gashin kai, shi ne kaɗai babbar nasarar da ya samu tun bayan hawan sa mulki, duk da haka ya ƙara da cewa amma fa Tinubu ɗin bai ma san irin ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da su ba.

“Wannan ɓaɓatu na baya-bayan nan da Sanata Ali Ndume ya yi, wanda ke wakiltar Barno ta Kudu, kuma Bulaliyar Majalisar Dattawa ta 10, wanda ya ce wai Shugaban ƙasa bai san halin matsalolin da ƙasar nan ke ciki ba, sun yi tsauri, kuma babu dalilin da zai feso wannan magana.

“A matsayin sa na sanata, Ndume ya na da dandamalin da zai yi magana kan wasu batutuwan da suka shafi alfanun ƙasar nan.

“Kuma ya na da damar ganawa da dukkan jami’ai Da hukumomin gwamnatin tarayya.” Cewar Kakakin Yaɗa Labarai na APC.

Morka ya ce abin damuwa ne tabbas idan Ndume ya yi ƙoƙarin ganin Shugaban ƙasa, amma abin ya gagara.

“To amma kuma hakan ba daidai ba ne da ya ce wai an kange Shugaban ƙasa. Kuma kasa ganawa da Tinubu ba dalili ko hujja ba ne da sanatan zai ce an kange Shugaban ƙasa daga sanin halin da ƙasar nan ke ciki.”

Ya ce Shugaban Ƙasa a ko da yaushe ya na cikin sha’anin al’amurran ayyukan ƙasar nan waɗanda ya maida hankali a kan su, kuma saboda su ɗin ne ma aka zaɓe shi.”

Daga nan ya ci gaba da lissafin wasu muhimman ayyukan da ya ce Tinubu ya gudanar da waɗanda ya zartas da kuma waɗanda ke gaban sa a yanzu.

By ukarofi