Kashi biyar ne kacal na mata ke riƙe da muƙaman siyasa a Nijeriya — Shugabar mata ta APC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugabar mata ta Jam’iyyar APC ta Ƙasa, Dakta Mary Idele Alile, ta ce kashi 5 cikin 100 ne kacal na mata a Nijeriya ke rikƙe da muƙaman siyasa.

Dr Mary ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin bunƙasa damarmakin mata a riƙa damawa da su a siyasa, wanda aka yi shi a Sakkwato a ƙarshen mako.

A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishinta, ta yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da ya ke yi na sauya yanayin ta hanyar baiwa mata muƙamai masu girma a manyan ma’aikatu.

Ta kuma yaba wa Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato bisa goyon bayan da yake bayarwa da kuma bayar da tallafin kuɗi ga shirin mai suna ‘Project 774 Eɗplode Initiatiɓe’ a jihar Sakkwato.

Ta ce, “Wannan shiri na da nufin ƙara ɗaukaka muryar mata a fagen siyasa da kuma ƙarfafawa ‘yan mata masu zuwa.”

Ta kuma nuna rashin jin daɗin ta ga yadda ta ce a halin yanzu akwai jihohi 15 babu wakilcin mace a majalisun dokokin su.

By ukarofi