Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana irin ƙoƙarin da ya ce APC ke yi domin ƙwace sauran jihohin Kudu maso Gabas daga hannun jam’iyyun adawa.
Ganduje ya ce APC ta kasa kama jihohin Enugu, Abiya da Anambra ne, saboda ‘yan yankin na yi wa shugabannin cikin APC kallon su na cikin waɗanda suka maida su saniyar-ware a siyasa da mulkin Nijeriya.
Ganduje ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi wurin taron Majiɓinta Lamarin APC na Yankin Kudu maso Gabas, a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi.
A Kudu maso Gabas dai jihohin Imo da Ebonyi ne kaɗai a hannun APC. Sauran Enugu, Abiya da Anambra kuwa su na ƙarƙashin PDP, LP da kuma APGA.
Ya shawarci shugabannin APC na Kudu maso Gabas su riƙa aiki tare cikin haɗin kai, domin APC ta karɓe sauran jihohin uku da ke hannun jam’iyyun adawa.
“Za mu karɓe sauran jihohin. APC ta kasa samun ɗimbin magoya baya a Kudu maso Gabas, saboda ‘yan yankin na yi wa shugabannin cikin jam’iyyar kallon cewa suna cikin waɗanda suka maida yankin su saniyar-ware a ƙasar nan,” inji Ganduje.
