Muna samun nasarar haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Jihar Kano – Hon Abdurrahman Salga

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jigo a fafutukar samar da haɗin kai domin tafiya ɗaya a Jam’iyyar PDP wanda ya yi wa jam’iyyar takarar neman majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Dala a zaɓen 2023, Hon Abdurrahman M Salga da aka fi Sani da Mai Nasara ya bayyana cewa kullum ƙudurinsa a rayuwa shine ya ga  matasa sun sami abin yi duba da irin abubuwa da ke faruwa a Kano akwai ƙalubale.

Ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen taron yaye matasa da aka koyawa gyaran waya a ƙarƙashin Bash communication.

Ya nuna cewa akwai zalunci irin tafiyar da shugabanin suke a yanzu, kullum abinda yake kira ga shugabanni shine bai kamata Allah ya damƙa musu wata dama da ya kamata su tsaya akan lamarin rayuwa na al’umma ba, musamman matasa amma su ƙi yin abinda ya kamata, idan har aka bari matasa suka lalace to gaba ɗaya za a rasa ci gaba a Arewa musamman idan aka  dubi  harkar daba dake faruwa a Kano.

Hon. Abdurrahman  M. Salga ya ce yanzu akwai wata Inuwa  da suka assasa da za su zauna da kwamiti a ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano  tareda masu unguwanni su ga ya ya za ayi a ɗauki matakai a magance matsalar daba da ake ta fama da ita a Kano, da  suka lura w rashin abin yine yake ingiza matasa su shiga da suna da abin yi ba za su shiga irin wannan hali na daba ba.

Ya ce a matsayinsa na matashi yana ƙoƙari ya bada gudunmawa a cikin wannan tafiya domin ba zai yiwu su zauna su zura Ido ba, donin  idan  suka koma ga Allah dole  zai  tambayi  irin abinda ka yi da ni’imar da Allah ya baka. Kar ka ce daga kai sai ya’yanka, ka fito ka ga cewa ka yaɗa ta ga al’umma sun ƙaru dakai. Allah bai ƙaddara cewa da talaka da mai arziƙi ɗaya bane, amma ka zama sanadin  zaman lafiyar al’umma da samun kwanciyar hankalinsu.

Hon Abdurrahman M. Salga ya yi nuni da cewa  shi a baya ba shi da ra’ayin siyasa a matsayinsa na ɗan kasuwa kuma mai neman na kansa da  ɗari da kwabo har gobe.Domin shi baya wani aiki na gwamnati da abinda ya mallaka ya fito domin ya taimakawa al’umma.Da  yaga cewa akwai haƙƙin su al’umma a harkar siyasa bisa lura  da  ana tura mutane  da  ba su cancanta ba shi ya sa ya shiga siyasa.

Ya ce shi a Abuja ya tashi sama da Shekaru 20 kenan da N1,500 ya tafi Allah ya kawo shi  matsayin da  yake yanzu saboda ya tafi da kyakkyawan zuciya shi ya sa siyasa da ya shiga ya zauna da ‘yan siyasa da yawa amma   sai ya lura cewa kowa ya yiwa magana, sai ya ga  fatansa daga shi sai ya’yansa. Mene ne amfanin hakan, bayan da matasa ake amfani  su basu ƙuri’a  su tafi su zalunce su su ci amanarsu.

Mai Nasara ya ce ya kamata a ce matasa su waye kar su zama ana amfani da su ana basu ƙwaya wannan ba abu ne mai amfani a  rayuwa ba.Duk ɗan siyasa da ya nema sai  ya ga bashi da tunanin a haɗa kai a taimaki al’umma,   amma akwai kaɗan waɗanda suke da tunanin yin hakan ya zauna da su da yardar Allah suna kan haka shi ya sa  shi ma ya fito ya ma tsaya takarar ɗan majalisar tarayya a zaɓe da ya gabata.

Ya ce sakamakon jagororin jam’iyyarsu na PDP sun rabu gida-gida sai ya ƙirƙiro wata Inuwa da za su haɗu gaba ɗaya da suka kira da PDP iyali ɗaya “PDP one family” gaba ɗaya jiga-jigan siyasa na Kano na PDP a zo a haɗu gaba ɗaya kar mutum yace ya ware  saboda kansa,  al’ummar zai duba.

Hon. Abdurrahman  M. Salga ya ce yanzu misali siyasa tana tahowa ta maganar shugaban ƙasa idan har al’umma da matasa suka fahimta cewa wanene a sama yafi karɓuwa a  takarar shugaban ƙasa to kar  aje a salwantar da ƙuri’a a inda ba za ta yi amfani ba.Wannan abin yake so ya nunawa al’umma musamman matasa an sami matsaloli a baya  wajen tsayar da shugabanni, yana so a zauna a duba idan har kasan cewa zaka tsaya takara ta Shugaban Ƙasa a iya Jihar Kano kaɗai za ka yi nasara, to ka haƙura da takara, ka duba al’umma ka bai wa wanda ya fika karɓuwa dama  idan ka salwantar da wannan ƙuri’a Allah sai ya tambayeka.

Ya ce  maganar da  yake ba ta son zuciya ba ce, idan aka ce yau Atiku Abubakar shine a gaba zai ɗau shugaban ƙasa daga Arewa to ko ɗan APGA ko NNPP ko APC ne a Arewa ya kamata ya  mara masa baya, karya duba cewa akwai bambancin  jam’iyya a samu ɗan Arewan dai ya hau da zai taimaki al’umma, duk da wasu sun hau sun ci amana amma da yardar Allah a gaba ba za a ci amana ba.

Hon. Abdurrahman M. Salga Mai Nasara ya ce a wannan fafutuka da yake na haɗa kan ‘yan jam’iyyar PDP a Jihar Kano ya sami haɗin Kan  yan jam’iyyar PDP sannan  kuma jagorori sun basu goyon baya yanzu ma har  jihohi irin su Legas, Bauchi, Jigawa duk sun ɗauka suna haɗa kan ‘yan jam’iyyar PDP a matsayin iyali ɗaya ba tareda bambancin gida-gida ba. Arewa in Allah ya yarda za a samu haɗin kai a tsaida mutum ɗaya wanda kowa yasan Atiku Abubakar ne a gaba in Allah ya yarda shine zai karɓi  shugabancin ƙasar nan.

By ukarofi