Ba ma fatan sake ganin shekara kamar wacce ta gabata – Sheikh Suleiman Na’ibi

Daga BALA KUKKURU a LEGAS

Na’ibin masallacin Juma’a na rukunin gidajen unguwar 1004, Tsibirin Biktoriya a Legas, Mahammadu Sadiq a ƙarƙashin jagorancin babban limamin masallacin, Sheikh Sulaiman Ibrahim ya bayyana cewa ba ya fatan ya sake ganin shekara irin ta bara. 

Na’ibin ya ƙara cewa, yana roƙon Allah Ubangiji Subahanahu Wa Ta’ala kada Allah ya sake maimaita wa har al’ummar arewacin Nijeriya da qasar nan bakiɗaya irin wannan shekarar da ta gabata. 

Shehin malamin ya yi wannan tsokaci ne a harabar masallacin jumma’a na unguwar 1004 jim kaɗan bayan kammala karatu tare da wa’azantar da al’umma bisa mahimmacin zaman lafiya. Inda kuma ya nuna damuwarsa a bisa ta’addanci da ya faru a cikin shekarar nan da ta gabata.

A cewar sa, al’amarin ya sanya ayyukan ta’addanci ya fi ƙarfi a waɗansu jihohin Arewacin Nijeriya kuma yake neman ya kawo cikas a noma da kasuwanci da sauran makamantansu. Inda ya bayyana cewa, duk da ya san irin ƙoƙarin da gwamnatin Nijeriya take yi a wajen kawo ƙarshen wannan al’amari, amma duk da haka yana ƙara shawartar gwamnatin da ta ƙara ƙoƙari a wajen kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar nan bakiɗaya.

Sannan ya shawarci al’ummar Nijeriya da su cigaba da ba wa gwamnati haɗin kai da goyan baya a lokacin da take gudanar da ayyukanta na kawo ƙarshen ta’addanci da sauran miyagun aiyukan da suke faruwa a cikin ƙasar nan bakiɗaya.

Daga ƙarshe ya yi wa al’ummar Nijeriya fatan alheri a game da shigowar sabuwar shekarar miladiya ta bana tare da fatan Allah ya kare dukkan jihohin Nijeriya daga faruwar irin waɗannan miyagun aiyukan da suke faruwa a cikin wannan sabuwar shekarar. Sannan ya jinjina wa babban limamin masallacin jumma’ar, Sheikh Malam Sulaiman Ibrahim a bisa ƙoƙarinsa na haɗa kawunan al’ummar musulmi domin cigaba da samun zaman lafiya da kwaciyar hankali mai ɗorewa a kowanne lokaci.