Messi na iya girgiza magoya bayan Barcelona a dalilin iyalansa

Ɗan wasa Lionel Messi zai iya dawowa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona sakamakon iyalansa basajin daɗin zama a babban birnin France Paris.

Iyalan ɗan wasan gaban ƙasar Argentina da Paris saint-german Lionel Messi sun bayyana masa ƙarara cewar ba su jin daɗin zama a babban birnin ƙasar Faransa wato Paris.

Iyalan na Lionel Messi sun fi jin daɗin zama a birnin Barca da ke ƙasar Sifaniya kafin subar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona.

A bayyane yake cewar Lionel Messi zai iya komai domin iyalansa kuma wannan dama ce da Barcelona za ta yi yunƙurin dawo da shi filin wasa na Camp Nou domin ya cigaba da fafata wasa.

Kwantaragin shekaru biyu ɗan wasa Lionel Messi yasan yawa Paris Saint-german acikin yarjejeniyar zamansa, Sai dai saboda iyalan ɗan wasan zai iya rage zaman nasa a ƙungiyar.

Lionel Messi ya nuna sha’awarsa na kammala wasan ƙwallon ƙafarsa a ƙasar Amurka, inda ake hasashen cewa yana gama kwantaraginsa a PSG zai koma can da taka Leda.

Jaridar El Nacional daga ƙasar Sifaniya ta bayyana cewar matar Lionel Messi Antonella Racuzza itace ta ke nuna rashin farin cikin ta kasancewarsu a birnin Paris.

Sai dai a cewar rahoton jaridar The Sun dan wasa Lionel Messi zai yi haƙurin kammala kwantaragin sa a PSG har nan da zuwa 2023 kafin ya ƙare ya koma Sifaniya.