Waye sabon shugaban Nijeriya a 2023?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Za a yi sabon babban zaɓe a Nijeriya a 2023 inda in Allah Ya yarda ranar 29 ga Mayun shekarar za a rantsar da sabon shugaba wanda zai karɓi madafun iko daga shugaba Muhammadu Buhari. An ƙara fahimtar lamarin a zantawa da aka yi da shugaba Buhari kwanan nan, inda ya ce, saura wata 17 ya rage a wa’adin gwamnatin sa, inda daga nan ya ce zai samu damar komawa Daura don kula da gonarsa. Shugaban dai wanda tsohon soja ne amma da alamu ya zaɓi komawa kula da gona bayan kammala aiki a fadar Aso Rock.

Duk da hakan ma ba wani baƙon abu ba ne wanda ya jagoranci Nijeriya ya koma gona ko don ma ya riƙa zuwa ya na jin kukan tsuntsaye da ganin bishiyoyi kamar yanda tsohon shugaba Obasanjo ya yi bayan barin mulki a 2007. A zahiri dai gonar irin waɗannan mutane waje na nishaɗi ko rage zafin kan rayuwa. Ko a tsohon shugaba Ibrahim Babangida an taɓa ganinsa yana yawo a gidansa da ke kan tsauni a Minna ya na duba shuke-shuke. Shi ma tsohon shugaba Abdulsalam Abubakar ya na da gona da kan samar da madarar da a kan zuba a masakan zamani a kai kasuwa.

Ku tuna min waye bai haɗa alaƙa da gona ba? Yauwa ai marigayi shugaba Umaru ’Yar’adua ma ya kula da gonar yayan sa marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’adua.

Ba mamaki motsawar magoya bayan mataimakin shugaba Buhari wato Yemi Osinbajo na ya tsaya takarar shugabanci, ya jawo masu niyya su ka yunƙuro don gwada sha’awar su ta takarar a jam’iyyar APC mai mulki.

Aƙalla dai an ga uban jam’iyyar Ahmed Bola Tinubu ya garzayo wajen shugaba Buhari inda ya sanar da shi ya na son yin takarar don kar a ce a kafafen labaru a ke jin burin na sa na son mulkar Nijeriya. Kazalika daga yankin Ibo an ga gwamnan da ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC wataƙila don samun takara gwamnan Ibonyi Dave Umahi ya sanar da aniyar takarar. Ba a bar tsohon gwamnan Abia Orji Uzo Kalu daga yankin na Ibo da ke cewa an hana shi damar shugabancin ƙasa fitowa ya bayyana aniyar takara ba. Ba wani ɓoyayyen abu ba ne tallar neman tikitin takarar da gwamnan Kogi Yahaya Bello ke yi. A makon jiya ma an samu wasu alarammomi da su ka taru a Kano su ka yi addu’a da mara baya ga Bellon da bayyana cewa ya burge su da bai hana mutane fit aba lokacin tsananin cutar Korona.

A PDP kuma tuni magoya bayan tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar su ka fito don nuna gwanin su zai sake gwada takarar. Maganar ma ta ƙara fitowa fili a wata ziyara da Atiku ya kai Gombe inda ya jagoranci taron ganawa da ‘yan kasuwa mai nuna bunƙasa harkokin kasuwanci a arewa maso gabar. Ba shakka da an buɗe harkokin kamfen da an fara jin bayanan takarar.

Hakanan a na ganin hotuna masu nuna niyyar takarar daga magoya bayan gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. A bara na ga mota ɗauke da rubutun da ke nuna niyyar takarar daga gwamnan PDP na Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad. Ba a rasa sauran masu niyyar takarar da ba su gama nazarin yin hakan ba irin tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

Tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido da kuma wanda ƙarfin sa ya bayyana amma ba ƙarin bayani a fili wato gwamnan Ribas Nyesom Wike. Babban abin da ya fi zama abin dubawa shi ne taqaddamar yankin da zai fito da dan takara a tsakanin kudanci da arewacin. Ga kudanci dukkan gwamnonin yankin ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, sun yi taro a Asaba jihar Delta inda su ka ce lalle yankin su ne zai yi takarar.

Wannan ya saɓa wa matsayar ‘yan siyasar arewa da ke cewa ba a tilasta zaɓen ɗan wani yanki a dole kuma ai dimokuraɗiyya da tsarin mulki ba su inganta batun mulkin karɓa-karɓa ba. ‘Yan Arewa na cewa duk mai son takara ya fito ya nemi goyon bayan sauran sassan ƙasa in ya so ƙuri’a ta yanke hukunci. Tunanin wasu ’yan siyasar kudu musamman maso yamma shi ne sun marawa shugaba Buhari baya, wanda ɗan Arewa ne ya yi mulki na tsawon wa’adi na biyu a yanzu da ya ke kammalawa, don haka yanzu lokacin ramawa kura aniyarta ne. Shin za a rama wa kura aniyar tata kuwa ko dai duk wanda ya iya allonsa ya wanke?

A yanzu dai alamu na nuna lamuran siyasar ta 2023 iya ruwa ne fidda kai. Gaskiya wannan batun na 2023 ke ƙara zafafa zaman tankiya tsakanin ‘yan Nijeriya. Ba ya ga kashe-kashe da ‘yan rajin Biyafara/IPOB ke yi, ga kuma masu kawo batun kafa ƙasar Oduduwa ta Yarbawa ƙarƙashin ɗan bangarsu Sunday Igboho.

Baba Ahmed ya nuna Arewa ba za ta sake kuskuren mara baya ga ɗan takara don zaman sa dan arewa kaɗai ba, matuƙar bai cancanci takarar ba. Kakakin ya ƙara da cewa, in Arewa ta samu takarar haka a ka fi so, amma duk wanda zai yi takarar sai ya samu mara baya don cancantar sa daga ‘yan Arewa da kuma ga ‘yan Nijeriya gaba ɗaya.

Wannan alama ce ta majalisar ba za ta duba sashin da ɗan takara ya fito ba, don dimokraɗiyya ba ta tilasta tsarin mulkin karɓa-karɓa ba.

Kazalika hakan ya sabawa manufar ƙungiyar ‘yan Arewa ta tsakiya masu cewa su ‘MIDDLEBELT’ ne da gwamnonin Kudu masu cewa lalle mulkin ya koma Kudu.

Majalisar Dattawan ta Arewa ta na son duk wanda zai zama ɗan takara ya mallaki kwarin gwiwa da dabarun inganta tsaro. A fili majalisar na nuna rashin gamsuwa ga kamun ludayin shugaba Muhammadu Buhari da ta ce bai ba wa marada kunya ba.

Tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Ango Abdullahi ke jagorantara majalisar da ke da mambobi da su ka haɗa da tsohon ɗan siyasa Tanko Yakasai da Ambasada Yahaya Kwande.

Ita kuma sabuwar ƙungiyar matasan dattawan Arewa ta ce duk wanda ya haura shekaru 60 a duniya ya hakura da takarar shugabanci a 2023 don ba zai samu goyon baya ba.

Sabuwar ƙungiyar mai mambobi a dukkan jihohin Arewa 19, ta gudanar da taro a Kaduna da naɗa shugabanni ƙarƙashin ɗan siyasa daga Bauchi Alhaji Umar Gital. A zantawa da kafar labaru ƙetare a Abuja, Alhaji Gital ya ce, duk shugabannin Nijeriya da su ka taɓuka abin kirki, sun samu damar shugabanci ne lokacin su na matasa daga shekara 30-40.

Gital ya ba da misali da Janar Gowon da ya dare mulki ya na wajajen shekara 30, Buhari a soja ya na wajen 40 hakanan ma shugaba Ibrahim Babangida.

A cewar Gital, hatta iyayen siyasar yankin arewa Ahmadu Bello Sardauna da Abubakar Tafawa Balewa sun samu hawa mulki sun a wajajen shekaru 50 a duniya.

Majalisar matasan dattawan ta ce, irin su Bola Ahmed Tinubu sun haura 70 hakanan tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar zai doshi shekaru 77 a lokacin zaven 2023.

Akwai buƙatar duk ’yan Nijeriya masu son ɗorewar zaman ƙasar a matsayin dunƙulalliya su maida zuciya nesa, su kaucewa nuna bambancin yanki da ƙabilanci don amfanin ƙasar. Wannan zaɓe na 2023 na da muhimmancin gaske don zai zo ne daidai lokacin da duk ɓangarorin siyasar Nijeriya sun hau karagar mulki an kuma ga tsarin su da fasahar su. Ma’ana gabanin 2015, jam’iyyar PDP ce ke kan karaga inda ta samu shekaru 16 ta na jan zare duk da taso ta yi 60 ne don zakin mulki.

Gamaiyar ‘yan adawa da ke ta gwagwarmaya tsawon shekaru ta samu lashe zaɓe inda shugaba Muhammadu Buhari ya ɗare karagar mulki. Don haka duk ɓangarori biyu sun yi zamanin adawa sun kuma yi zamanin mulki. Sun cika alkawari ko ba su cika alƙawari ba, jama’ar ƙasa masu zaɓe su ne alƙalai matuƙar ƙuri’a za ta yi aiki. Har yau dai na daga matsalolin Nijeriya rashin wadatar lantarki, rashin ingantattun asibitoci tun da shugabanni da masu kuɗi a turai su ke zuwa jinya.

Batun rashin tsaro ya zama tamkar ruwan dare don masu satar mutane a Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya sun zama a yanzu a na ambatar su da su ma ‘yan ta’adda ne kamar ‘yan Boko Haram a Arewa maso gabas. Titunan mota ba su gyaru ba don a wasu titunan matuƙar mutum bai yi hankali ba sai ya fasa taya a ‘yar tafiya tsakanin jihohi biyu. Talauci kuma bai taɓa zama tarihi ba a tsakanin talakawa don kusan duk shekara sai ka ji a na cewa gara bara da bana.

Yiwuwar tashin farashin man fetur na nan matuƙar gwamnati ta jnaye dukkan tallafi. Hakanan dala kullum tsada ta ke yi da hakan kan ƙara tada farashin kayan masarufi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *