Ba ma goyon bayan Kawu Sumaila kan munanan kalamai wa shugaban jam’iyyar NNPP – KYD

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙungiyar Cigaban Matasa a Siyasar Kano, wato Kano Youth Democrat, Malam Aliyu  Sumaila ya yi tir da matakin rashin biyayya da Sanatan Kano ta Kudu ya ɗauka kan Shugaban Jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa duk da cewa jagorancin jam’iyyar gaba yake da duk wani me riƙe da kujerar siyasa a ƙasa.

Sumaila ya ce sun yi mamaki mutuƙar gaske ganin yadda Sanata Kawu Sumaila ya ke aibata shugaban jamiiyar NNPP a kafafen yaɗa labarai ganin cewa jam’iyya tana da damar ladabtar da duk wani ɗan ta da ya kauce daga manofofin tafiyarta.

Ya ce “A tsarin siyasar ƙasar nan duk wani ɗan jam’iyya da ya samu saɓani da wani a jam’iyya, uwar jam’iyyar ce take shiga tsakani, saboda haka maganar da Dungurawa ya yi kan tsawatarwa  Kawu Sumaila akan  ya daina shiga mahibban jagoran jam’yyar NNPP na ƙasa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Kano abu ne da ke kan tsarin doka na tafiyar Kwankwasiyya.”

Shugaban na KYD ya ƙara da cewa, Sanata Kawu Sumaila ya tuna cewa al’umma ba su zaɓe shi ba sai da jam’iyyar NNPP ta hasale masa ya yi takara a cikinta kuma sunan jam’iyar har yau yake amfani a majalisar dokoki na ƙasa, hakan na nuwa cewa jam’iyya ce gaba da kowa a muƙamin da mutum ya tsinci kansa akai zaɓaɓɓe.

Aliyu Sumaila ya ƙara da bayyana cewa idan dai ba Sanata Kawu Sumaila yana da wata manufa  na daban ba kan shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano ya gaggauta janye ƙaran da ya shigar kotu domin samun maslaha da cigaban jam’iyyar a Kano ta Kudu.

Ya ce suna sane da wata ƙulalliyar tsari da aka ɗauko domin wargaza haɗin kan jamiyar NNPP da take da shi a Kano domin biyan buƙatun wasu a Abuja, lokaci zai zo da zamu bayyana ma al’umma irin shirin da maƙiya cigaban jihar Kano suka ɗauko domin kassara tafiyar Gwamnatin Abba Gida-gida da jagoran jam’yyar na ƙasa baki ɗaya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a cewar Sumaila.

“A ƙarshe ƙungiyar “KYD” da kuma tafiyar jam’iyyar NNPP a shiyar Kano ta Kudu ba ma goyon bayan Sanata Kawu Sumaila kan matakin da ya ɗauka kan shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, mu masu biyayya ne da tsarin uwar jam’iyya na ƙasa da jiha baki ɗaya,” cewar Aliyu Sumaila.