Ba ma son Nijeriya ta zama mai jam’iyya ɗaya – Gwamna Sule

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ba ta son zama jam’iyya ɗaya a ƙasar.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Talata bayan wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce ya je ne domin tattauna batutuwan da suka shafi jihar da kuma jam’iyyar APC.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan yanayin siyasa a ƙasar da kuma damuwa da ɓangaren adawa ke nunawa cewa ƙasar ta doshi zama mai jam’iyya ɗaya, gwamna Sule ya ce APC na son jam’iyyar da ke sahun gaba a ƙasar ne kaɗai, wadda za ta iya lashe zaɓuka.

Ya kuma yi iƙirarin cewa batun canza sheƙa da ake ta yi, musamman zuwa jam’iyyar APC – na faruwa saboda irin ƙokari da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi, inda ya ce “hakan manuniya ce ta ƙwazon jam’iyyar APC da kuma Tinubu. Shugaban ƙasa na kawo sauye-sauye da dama. Mun ga wasu daga cikinsu.”

“Ban amince cewa za mu iya zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba. Ida ka duba batun, kowace irin nasara za mu samu, hakan ba za ta faru ba, alal misali ga jam’iyyar Republican a Amurka da kuma Democra. Akwai jam’iyyar Green da kuma wasu da dama da ba ka jin labarinsu. Haka batun yake a Nijeriya,” inji Gwamna Sule.

By ukarofi