Hanyoyin gane kasuwancin damfara na zamani da matakan kiyaye su 

Spread the love

A wasu shekaru da suka gabata, da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun yi asarar dukiyoyin su da kuɗaɗen ajiyarsu da niyyar bunƙasa su ta hanyoyin kasuwancin zamani. Manajojin kafafen kasuwancin zamani sun wawushe kuɗaɗe na kimanin biliyoyin Naira daga gumin al’umma ta hanyoyin damfara. Kasuwancin damfara ta hanyar zamani wani irin kasuwanci ne da ake wa waɗanda suka zuba jarinsu a ciki alƙawarin riba mai ɗimbin yawa ba tare da wata wahala ko asara ba. Daga cikin waɗannan hanyoyin kasuwanci na zamani akwai irinsu MMM, Get Help Worldwide da kuma CBEɗ. Suna gudanar da kasuwancin su ne ta hanyar amfani da jarin kostoma ‘sabon shiga’ domin biyan tsohon kostoma. 

Abin takaici ne yadda waɗannan dabarun kasuwanci na zamani ta hanyar damfara suka zama ruwan dare a cikin al’umma. Waɗannan hanyoyin zuba jari na cigaba da bunƙasa a kowacce rana. Suna amfani da kalmomi ko sunaye na turanci masu jan hankali domin damfarar mutane. Muhimman dalilan da ke sa mutane faɗawa cikin wannan damfaran sun haɗa da kwaɗayin tara abin duniya, da burin zama hamshaƙan masu kuɗi a ƙanƙanin lokaci, talauci, rashin ilimi da kuma rashin ƙwaƙƙwaran aikin yi ga matasa da sauran su.

Abin haushi, a wasu makonnin da suka gabata, bayan ɓarayin zamani na CBEɗ sun damfari jama’a kuɗaɗen su, wannan damfarar ta janyo cece-kuce a cikin ƙasa, kuma ya sanya waɗanda aka damfara zama abin tausayi. An yi hasashen cewa mutanen sun rasa kimanin tiriliyan 1.3 na harkokin kasuwancin su, sakamakon damfarar CBEɗ. Jaridar Turanci ta ɓanguard ta rawaito cewa wasu ma’aurata biyu sun zuba dala dubu bakwai kimanin miliyan ɗaya in aka juya ta zuwa Naira. Sun yi asarar wannan kuɗin ajiyarsu ta hanyar CBEɗ. A halin yanzu, suna cikin takaici, damuwa, baƙinciki da matsin rayuwa. 

Hakazalika, wani likita shi ma ya yi asarar kuɗinsa ta hanyar wannan kasuwanci na damfara. Likitan wanda ke aiki a asbiti yanzu yana fama da ciwon zuciya. Wata mata ta karɓi bashin wasu kuɗaɗe masu yawa ta zuba jarin a CBEɗ, da ta ji labarin cewa waɗannan barayin zamani sun wawushe mata kuɗinta, baƙin ciki da takaici ya saka ta rataye kanta, ta mutu. Da yawa a cikinsu sun zuba kuɗaɗen su domin ta bunƙasa kasuwancinta, kuma ta biya wasu buƙatun rayuwa. Amma maimakon ta fashe sai ta yi bindiga da masu jarinta.

Kasuwancin zamani na damfara na da iloli da yawa ga masu yi da kuma al’umma. Illar hakan ga mai yi shi ne yana janyo masa asarar dukiya. Sa’annan asarar dukiyar na kawo wa zuciya ƙunci da baƙin ciki kuma tana iya janyo wa mutum mutuwar wuri a ƙanƙanin lokaci. Hakan nan, hasarar dukiya ta hanyar damfara na janyo mummunan tasiri ga karatun yara, kiwon lafiya da kuma mutuncin su da sauran buƙatun rayuwa. Kuma yana kawo rashin jituwa da kuma durƙushewar amana a tsakanin mutane. Illar ta ga al’umma yana janyo tashin hankali da rashin natsuwa ga mutane wacce za ta iya tada zaune tsaye in ba a kiyaye ba.

Wannan dabarar kasuwanci na daga cikin  tsofaffin hanyoyin kasuwanci na rashin gaskiya, da yaɗu a wurare daban-daban. Ana yi wa ire-iren wannan kasuwanci laƙabi da Turanci “Ponzi Scheme.” Ta samo asali ne daga wani mutum mai suna “Charles Ponzi” wanda shi ya fara kafa irin wannan salon kasuwancin na damfara a shekarar 1920, inda ya riƙa gudanar da kasuwancin ta hanyar biyan tsofaffin kostomomi daga jarin sabbin kostomomi. Lokacin da kasuwancin ya fara durƙushewa sai sabbin kostomomi suka daina zuba jarin su a ciki, inda aka shiga rasa masu zuba hannun jarinsu a kasuwancin.

An ƙirƙiro da manhajar CBEɗ ta damfara ne a watan Yuli cikin shekara 2024, kuma an kafa ofishin ta a garin Ibadan na Jihar Oyo. Ma’aikatan sun kasance suna tallata kasuwancin kamfanin sun riƙa cewa za su bai wa duk wanda ya zuba jarinsa a CBEɗ ribar kashi dari da kuma yin alƙawari ga duk wanda ya kawo sabbin kostoma wani kaso na tukwici. Masu bincike sun gano cewa CBEɗ ba ta yi rijista da Ma’aikatar Kula da Kasuwancin Zamani mai suna ‘Securities and Eɗchange Commission’. Sannan an gano cewa sun sace sunan CBEɗ ne daga wani kamfanin ƙasar China mai suna, ‘China Beijing Eƙuity Eɗchange’. Amma wannan kamfanin ya ƙaryata duk wata dangantaka tsakanin sa da CBEɗ na Nijeriya.

Masana sun yi bayani kan matakan da mutane za su kiyaye faɗawa cikin irin wannan kasuwanci na damfara. Daga ciki akwai zurfafa bincike ta hanyar tambayar masana akan ingancin kowanne irin kasuwancin zamani, kafin mutum ya zuba jarinsa a ciki. Dukkan kasuwancin da ake alƙawarin riba mai yawa yakamata mutum ya yi taka tsantsan da shi. Dukkan kasuwancin da ba a yi masa rijista da ma’aikatar mai kula da kasuwancin zamani ta ‘Securities and Eɗchange Commission,” ko wata hukuma mai alaƙa da haka ba, bai kamata kowa ya zuba jarinsa a ciki ba, domin kaucewa faɗawa tarkon ’yan damfara. Ga shafin da ya kamata mutum ya yi bincike kan kasuwancin zamani aka yi wa rijista kafin zuba jari a ciki. “https://www.sec.goɓ.ng/cmos/

Harwayau, duk kasuwancin zamanin da mutum bai gane takamaiman yadda ake gudanar da shi ba, ko kuma yadda ake samun riba a cikinsa ba, gwara ya haƙura. Duk wani tallen kasuwancin zamani da ba za a iya gamsar da mutum akan yanayin yadda ake gudanar da shi cikin minti biyar ba,  gara a hakura da shi.

Ya kamata hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci su wayar wa mutane kai akan illolin zuba jari a kasuwancin zamani masu ƙunshe da damfara. Gwamnatin Tarayya ta sanya doka mai tsanani ga duk masu damfarar mutane kuɗaɗensu. Harwayau, ba kowanne ɗan kasuwa yakamata a bari yana shigowa Nijeriya da sunan tallata kasuwancin zamani ba. Kafin a bari, dole a gudanar da binciken ƙeƙe-da-ƙeƙe. Malamai su riƙa yi wa mabiyansu nasiha akan amfanin wadatar zuciya, da haƙuri da ƙanƙanuwar riba, mai albarka. Sannan yakamata Hukumar EFCC ta bi wa duk wani ɗan Nijeriya da ma’aikatan CBEɗ suka damfara haƙƙinsa.

Allah Ya taƙaita mana masifu, Ya kuma shige mana gaba a harkokinmu. Allah Ya azurta mu maza da mata da dukiya masu albarka, Ya kuma zaunar da ƙasar mu lafiya. Amin. 

Daga Hassan Imran, wanda ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa na imel: [email protected].

By ukarofi