Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El- Rufai ya ce ba zai yi gudun hijira ba duk da raɗe-raɗin da ake yi na cewa ana shirin kama shi tare da azabtar da shi.
El-Rufai ya faɗi haka ne a martanin da ya mayar a shafinsa na ɗ bayan wani mai amfani da shafin ya wallafa cewa ya samu bayanai masu ƙarfi da ke nuna ana shirin kama El Rufai.
”Na daɗe ina jin waɗannan raɗe-raɗin kan kama ni da tsare ni da kuma azabtar da ni a wani ɗakin azabtarwa da ke ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (wurin da ake zargin an azabtar ta Emefiele domin ya bar aiki a matsayin gwamnan CBN), tun watan Yulin 2024 lokacin da aka fara yaɗa rahoton majalisar dokokin jihar Kaduna,” inji shi.
Ya kuma ce an aika irin waɗannan saƙonnin barazanar ta hanyar abokai da ‘yan uwan shi da dama saboda ana so ya yi ji tsoro ya yi gudun hijra da kan shi, sai dai El Rufai ya ce ”ba zan yi hakan ba”.
Ya ce kafin ranar 20 ga watan Fabrairu zai dawo Nijeriya, ya kuma ce ya dakatar da karatun da yake yi da kuma shirin koyon wasu harsuna zai dawo gida Nijeriya, domin a cewarsa ba zai ci gaba da yin shiru ba.
El-Rufai ya kuma ce kamawa da tsarewa da kuma azabtar da abokan hamayya a siyasa ba sabon abu ba ne, ”ni kaina an kama ni kuma an kulle ni sau uku a baya saboda bayyana ra’ayi na kan gwamnatocin baya,” a cewarsa.
A ‘yan kwanakin nan dai ana ta samun ce-ce-ku-ce tsakanin tsohon gwamnan Kaduna El-Rufai da ‘ya’yan jam’iyya mai mulki na APC da kuma rashin jituwa da ake zargin akwai tsakaninsa da gwamnan jihar na yanzu Uba Sani.