Dalilin da ya sa ba zan sulhunta mahaifina da Gwamna Uba Sani ba — Bello El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dan majalisar da ke wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Arewa a Majalisar Wakilai, Bello El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai iya sulhunta mahaifinsa, Nasir El-Rufai, da Gwamna Uba Sani kan rikicinsu na siyasa da ke ci gaba da gudana ba.

A cewarsa, warware saɓanin siyasar tsoffin abokan tafiyar ba aikinsa ba ne a matsayin ɗan majalisa.

Haka zalika, ya bayyana cewa binciken da ake yi wa gwamnatin El-Rufai da ta shuɗe ba wani abu mai illa ba ne.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa a tabbatar ana yin binciken da kyakkyawan niyya.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, wanda aka gabatar a ranar Asabar.

“Ba aikina ba ne. Aikina shi ne in mai da hankali wajen cika alƙawuran da na ɗauka ga al’ummar Kaduna ta Arewa. Ina kaunar zaman lafiya da gaskiya. Amma a wurina, idan zan yi magana kan wata matsala, sai in bi ta hanyar da ba ta bayyana ba.”

“A wurina, babu wani mutum da na sani a siyasa kamar Malam Nasiru. Tun ina ƙarami ya kasance mashawarcina, kuma hakan zai ci gaba har abada,” inji shi