Bismillahi rahmanir Rahim. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da ɗaukaka, wanda sanya Muminai ’yan uwan juna, sashinsu na taimakon sashi. Salati da sallama su ƙara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har zuwa ranar sakamako.
Lalle ne ‘yan uwantaka tsakanin mutane a addini bai taƙaita ga Musulmai kaɗai ba, har ga waɗanda ba Musulmai ba sukan zama ‘yan uwa a addininsu, amma yan uwantaka ta Musulunci ya fi kowani irin ‘yan uwantaka, saboda shi ‘yan uwantaka ne akan addinin gaskiya, kuma alaƙar ɓata yankewa har bayan mutuwa. Allah Madaukakin sarki ya ce: “Masoya a wannan yinin abokan gaban juna ne, face masu takawa”. Suratuz Zukhruf: 67.
Haƙiƙa Allah Ya sanya yan uwantaka ta Musulunci ta fi yan uwantaka ta jini, kuma ya shar’anta son junansu da kuma yin duk abinda zai ƙarfafa yan uwantaka a tsakanin su, saboda da hakan ne addini zai tsayu, kuma a samu taimakekeniya a tsakanin Musulmai.
Haka kuma Allah Ya hana duk wani abinda zai ɓata yan uwantaka, zai kawo saɓani a tsakanin musulmai. Allah Ya ce: “Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni’imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance maƙiya, sai Ya sanya soyayya a tsakaninku, saboda haka kuka wayi gari da ni’imarsa ‘yan uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar haka Allah Ya ke bayyana muku rayoyinsa, tsammaninku za ku samu shiryuwa”. Suratu Al ‘Imran: 103.
’Yan uwantakan Musulunci ɓata tsaya lokacin zaman lafiya tsakanin Musulmai ba, har ma lokacin faɗa da juna suna nan a matsayin ’, ’yan uwan juna, kamar yadda Allah Ya ce: “Kuma idan jama’a biyu ta muminai suka yi yaƙi, to ku yi sulhu a tsakaninsu,” har zuwa inda Allah Ya ce: “Abin sani kawai muminai ’yan uwan juna ne, saboda haka ku yi sulhu a tsakanin ’yan uwanku biyu”. Suratul Hujurat: 9-10
Musulunci ya wajabtawa Musulmai idan sun haɗu da junansu su yiwa junansu sallama. Saboda sallama tana ƙarfafa imani, wanda shine sababin shiga aljanna. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wallahi ba zaku shiga aljanna ba har sai kun yi imani. Kuma ba zaku yi imani ba har sai kun so junan ku. Shin baku so in nuna muku abinda in kuka yi shi zaku so junan ku? Ku yaɗa sallama a tsakaninku”.
Kuma Muslunci ya hana Musulmi ya ƙauracewa dan uwansa musulmi, saboda hakan zai haifar da kiyayya da gaba a tsakaninsu, sai in ya zama ƙauracewar saboda yana aikata wani sabo ne.
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Musulmi dan uwa Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya miƙa shi ga halaka, duk wanda ya biyawa ɗan uwansa buƙatunsa, to Allah zai biya masa buƙatunsa. Duk wanda ya yaye wa Musulmi baƙin ciki, to Allah zai yaye masa bakin cikin ranar al-kiyama. Duk wanda ya suturce wani Musulmi, to Allah zai suturce shi rananr al-kiyama”.
Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ana bijiro da ayyuka (ga Allah) a duk ranar alhamis da litinin, sai Allah Ya gafarta a wannan ranar duk mutumin da baya shirka, sai mutumin da ya kasance akwai gaba a tsakanin shi da ɗan uwan shi, sai a ce: Ku jinkirtawa waɗannan har sai sun yi sulhu, ku jinkirtawa waɗannan har sai sun yi sulhu”.
Saboda haka Musulunci ya haramta Musulmi ya ƙauracewa ɗan uwansa fiye da kwanaki uku kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya faɗa: “Bai halatta musulmi ya ƙauracewa ɗan uwan sa ba fiye da kwana uku, su haɗu da juna, wannan ya juya baya, wannan ma ya juya baya, kuma mafi alherinsu shine wanda kuma mafi alherinsu shine wanda ya fara yin sallama”.
Allah maɗaukakin sarki Ya haɗa mu akan tafarkin gaskiya, Ya kuma cire duk wani gaba da ƙulli a tsakainmu.
Daga DAN UWANKU AL-MUNTAZAR. 09070905293.