Ba zan miƙa jami’o’in Gwamnatin Tarayya ga jihohi ba – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar Shugaba Nijeriya a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai miƙa wa gwamnatocin jihohin ƙasar ragamar tafiyar da jami’o’in gwamnatin tarayya ba.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar ya ce sun lura cewa an juya maganar da ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na ƙungiyar lauyoyin Nijeriya da ya gudana a Legas a kan batun da ya shafi ɓangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da ɓangaren ke fuskanta.

Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai miƙa ragamar kula da jami’o’in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zaɓe shi a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Wannan ba daidai ba ne don bai faɗi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa, inji shi.

Ya ce abin da Atiku Abubkar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami’o’in da ke ƙarƙashinta.

A don haka batun cewa zai miƙa wa gwamnatocin jihohi ragamar tafiyar da jami’o’i ba gaskiya ba ne.