Mun danƙara wa jami’an tsaro isassun kuɗaɗe – Hon. Alhassan Doguwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Tarayya, Alasan Ado Doguwa, ya bayyana cewa Majalisar Tarayya ta danqara wa jami’an tsaron Nijeriya musamman sojoji wadatattun kuɗaɗen da duk ta ke buƙata wajen daƙile matsalar tsaro.

Doguwa ya yi wannan iƙirarin ne a ranar Lahadi, lokacin da ya ke kaɓar kyautar karramawa daga ƙungiyar Kano Citizens Forum.

Ya ce harkar tsaro abu ne mai muhimmanci sosai wanda majalisa kwata-kwata ba ta wasa da shi.

Sauran waɗanda aka karrama a wurin sun haɗa da tsohon Kwamandan Burget ta 3 da ke Kano, Sinyinah Nicodemus da kuma Kamshinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Dikko.

Doguwa ya ce aikin tsaro na buƙatar haɗin kai da goyon bayan dukkan ‘yan ƙasar nan, saboda ba kowa ne zai iya fita daji ya tunkari ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ba, sai jami’an tsaro.

“Saboda su na buƙatar goyon baya da addu’o’i. Nasarar su nasarar mu ce baki ɗaya. Kuma gazawar su gazawar ƙasar ce da ‘yan ƙasar baki ɗaya.”

Doguwa ya ce, “saboda muhimmancin tsaro ya sa a majalisa mu na da wata ƙa’ida cewa ba mu tava kasafin kuɗin tsaro, wato mu yi masa kwaskwarima ko mu rage shi. “Dukkanin mu mun amince cewa kada mu riqa yin shisshigi a cikin kuɗaɗen fannin tsaro. Duk abin da aka tambaya, mu na amincewa a ba su.”

Ya roƙi ‘yan Nijeriya su ci gaba da nuna goyon baya ga jami’an tsaro musamman ta hanyar yi masu addu’o’in samun nasara.