Babba Kaita ya jajanta wa ɗaliban sakandire na Ɓatagarawa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita ya jajanta ma ɗaliban makarantar sakandare na Government Science Secondary School Ɓatagarawa, iyayen su da al’ummar Ɓatagarawa ta jihar Katsina game da ibtila’in da ya faɗa ma ɗaliban wanda ya shafi lafiyar ɗalibai sama da sittin (60).

Duk da cewa rahotanni na zuwa daga majiya daban daban, jaridar Daily Trust ta yau, 27/10/2026 ta wallafa cewa ibtila’in ya biyo bayan shan maganin da aka ce na fitsarin jini ne wanda jami’an kiwon lafiya suka ba ɗaliban.

Jaridar ta ƙara da baiyana cewa kwamishinan ilimi na jihar ya tabbatar da ibtila’in har ma da cewa an kai yaran asibiti kuma ana kulawa da su sittin da biyar.

Babban sakataren yaɗa labarai na ɗan takarar Malam Ahmed Abubakar ya fitar, Babba Kaita ya nuna damuwar sa yadda matsalar musamman idan an yi la’akari da bidiyon da ke yawo a yanar gizo inda a ke ganin yanda wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ko motsi ba su yi, ga su nan zube a ƙasa a asibitin.

Ɗan takarar ya kushe lamarin da kakkausan murya da kira ga gwamnati tare da dukkan hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta bincike da hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan gangancin don kiyaye gaba.

Ya kuma yi kira da a gaggauta ganowa da kuma ɗaukan matakan da suka dace a dukkan wasu wuraren da aka kai irin wannan maganin cikin makarantu da al’ummomi musamman na karkara.

Ya roƙi Allah da ya ba waɗanda abin ya shafa lafiya ya kuma kiyaye aukuwar irin wannan tashin hankalin a gaba.

Ya zuwa yanzu bayanai na nuna suna cikin ƙoshin lafiya bayan da suka sami kulawar malaman asibiti.

By ukarofi

Leave a Reply