Babban hafsan tsaro ya ƙarfafa alaƙar tsaron Nijeriya da Amurka

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, ya ƙarfafa alaƙar tsaron Nijeriya da ƙasar Amurka yayin ganawar da ya yi da Janar Charles Brown JR, Babban Hafsan Tsaron Amurka. 

Taron dai ya gudana ne a gefen taron hafsoshin tsaron ƙasashen Afrika, wanda USAFRICOM da rundunar tsaron Botswana suka shirya.

A cewar Birgediya Janar Tukur Gusau, Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, taron ya yi matuƙar amfani, kuma an lalubo hanyoyin da za su amfanar da juna.

Ya ce, Janar Musa ya kasance babban mai gabatar da jawabi a taron kan “Wanzar da zaman lafiya, yaƙi da ta’addanci, da kuma ayyukan magance rikice-rikice,” yana mai jaddada muhimmancin hacin gwiwa da amfani da fasaha wajen yaƙar ta’addanci.

A taron, an kuma tattaunawa batun samar da haɗin kai a tsakanin hafsoshin tsaron Afirka da kuma inganta shirye-shiryen gudanar da ayyuka ta hanyoyin da suka dace don yaƙar rashin tsaro a nahiyar.

Shugaban ƙasar Botswana, Dokta Mokgwetsi Eric Keanetswe Masisi ne ya buɗe taron mai taken “Faɗaɗa Haɗin Kai” a hukumance, inda ƙasashe 42 suka halarta.

Janar Musa ya bada gudummawa wajen tattaunawa kan wanzar da zaman lafiya.

An ruwaito cewa, wannan taro ya ƙara tabbatar da aniyar Janar Musa na yin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe wajen tunkarar ƙalubalen tsaro a yayin da sojojin Nijeriya ke ci gaba da jajircewa wajen kare muradun ƙasa da kuma inganta tsaron yankin.

By ukarofi