Sojoji sun ƙwato makamai daga hannun ’yan ta’adda a Filato da Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Dakarun Operation SAFE HAVEN na rundunar Sojojin Nijeriya sun kama wasu mashahuran ’yan bindiga, masu safarar makamai da kuma ƙwato makamai a wasu ayyukan sirri da suka gudanar a jihohin Filato da Kaduna cikin mako guda da ya wuce.

A ranar 21 ga watan Yunin 2024, sojoji sun gudanar da wani samame na fatattakar ‘yan bindiga da wasu masu aikata laifuka a maɓoyarsu da ke dajin Pandam a ƙaramar hukumar Ƙua’anpan ta Jihar Filato.

A yayin samamen, sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3, cinkun alburusan AK-47 guda 5 da harsashi 75 mai tsawon 7.62mm (na musamman).

Bugu da ƙari, a wani samame tare da sauran hukumomin tsaro a ranar 21 ga watan Yunin 2024, sojoji sun bindige tare da kama wani ɗan bindiga da ya addabi hanyar Riyom zuwa Abuja a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.

An kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta bayar da cinkun alburusan AK-47 guda 35 ga wani ɗan bindiga. Amma an bi sawun sa aka kama shi a jihar Kano a ranar 20 ga watan Yunin 2024. 

Ƙarin bayani da aka samu daga wanda ake zargin ya kai ga kama babban mai sayar da makamai a Manchok da ke ƙaramar hukumar Kaura a Kaduna, yayin da ake ƙoƙarin karɓar cinkun alburusan AK-47 guda 35 daga hannun ɗan bindiga na farko domin kai wa ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Sojojin sun ci gaba da bincike a gidan babban ɗan bindigar inda suka kwato cinkun alburusan AK-47 guda 35 da babura ƙirar Bajaj guda 3, wayoyin hannu 3 da kuma wasu kayayyakin.

Jama’a na yaba wa da baiwa jami’an tsaro sahihan bayanai da suka kai ga wannan nasara. An kuma yi kira ga al’ummar ƙasar da su ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai wajen tabbatar da tsaro a Nijeriya bakiɗaya.

By ukarofi