Yadda Tinubu ya ke so na sauke nauyin da ya ɗora min – Idris

Spread the love

Ministan yaɗa labaria da wayar da kan al’umma, Alhaji Mohammed Idris, yace shugaba Tinubu ya umarce shi da dawo da yadda daga al’umma wajen yin aikinsa.

Idris ya faɗi haka ne a Abuja yayin taron bikin shekara 60 na “National Institute of Public Relations”.

Ya cigaba da cewa, na samu sahalewa da kuma albarkar maigidana, Shugaba Bola Tinubu, wanda ya naɗa ni domin dawo da martabar sadarwa ga jama’a.

Ya ƙara da cewa dole a dawo da gaskiya da amana wajen sadarwa, domin ta wannan ne kaɗai yan ƙasa zasu yadda da gwamnati.

Ministan ya ɗau alwashin cigaba da yin haka, har sai aikin sa ya ƙare. Ya ƙara da cewa dole a dawo da yarda wajen sadarwa ga al’umma.

Shiyasa idan ban da bayani a kan wani abu, sai ince banda shi.

By ukarofi