Babban taro: INEC ta ankarar da APC wasu dokoki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi fatali da wasiƙar gayyata zuwa wajen taron Majalisar Zartaswa (NEC) na gaggawa na jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi watsi da takardar ne saboda ba ta ga sa hannun Shugaban Riƙon Jam’iyyar APC da na Sakataren sa ba.

Da yiwuwar yunƙurin cire Mai Mala Buni ƙarfi da yaji ya haifar da matsala a babban taron ƙasa da jam’iyyar ta shirya za ta yi a ƙarshen watan Maris ɗin nan.

INEC, a wasiƙar da ta aike ranar 9 ga Maris, 2022 kuma sakatarenta, Rose Oriaran Anthony, ta rattaɓa hannu, hukumar ta ce APC ta saɓa ƙa’idar sashe na 1.1.3 na dokokin ayyukan jam’iyyun siyasa.

INEC ta ƙara da cewa bisa sashe na 82(1) na dokar zaɓe, akwai buƙatar a sanar da ita ana saura kwanaki 21 aƙalla kafin wani babban taro, ko ganawa don maja da zaɓen sabbin shugabanninta.

INEC ta bayyana wa APC cewa saboda haka ta yi watsi da wasiƙar; kamar dai yadda sashen wasiƙar ke cewa, “Hukumar na janyo hankalinku kan cewa shugaban jam’iyya da sakatare ba su rattaɓa hannu kan zaman majalisar ba, kuma wannan ya saɓa wa sashe na 1.1.3 na ƙa’idojin harkokin jam’iyyu (2018).

“Bayan haka, muna tuna wa APC sashe na 82(1) na dokar zaɓen 2022 wanda ke buƙatar sanar da hukumar kan wani taro, ganawa, ko zama don niyyar zaɓen shugabanni ana saura aƙalla kwanaki 21.”

Ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta tashi cikin ruɗani, inda aka ga Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya ɗare kujerar shugabancin riƙon jam’iyyar na ƙasa, har kuma ya rantsar da shugabannin kwamitin da za su jagoranci shirya babban taron jam’iyyar da za a yi.

Lamarin da ya haddasa cacar baki tsakanin Gwamna Mai Mala Buni da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai, wanda ya fito a gidan talabijin na Channel ya bayyana cewa “Mai Mala Buni ya yi bankwana da shugabancin jam’iyyar APC.”