Gwamnatin Tarayya ta horas da matasa kan dabarun kula da abincin ‘yan gudun hijira a Keffi

Daga BASHIR ISAH

A ranar Larabar da ta gabata Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Waɗanda Rikici ya Ɗaiɗaita (NCFRMI) ta kammala shirin horar da gomman matasa a garin Keffi, jihar Nasarawa kan dabarun girke-girke don amfanin waɗanda rikici ya ɗaiɗaita.

Shirin ya gudana ne a ƙarƙashin kulawar Kwamishinar Tarayya a ma’aikatar NCFRMI, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, inda aka horas da matasa kan dabarun sarrafa abinci ga waɗanda rikici ya ɗaiɗaita da suke zaune a garin Keffi.

Shirin bada horon ya gudana ne na tsawon kwanaki biyar, wanda bayan kammalawa aka miƙa wa kowannensu shahadarsa tare da kayan aiki da kuma tallafin kuɗi Naira 20,000 ga kowannensu.

Shirin bada horon da kuma bikin yayewar sun gudana ne a babban zauren taron Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi.

Da yake jawabi a wajen taron, wakilin Kwamishina Imaan, Mr Tunde Oyasanya wanda mataimakin darakta ne a hukumar, ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Shugaba Buhari na bada tallafi ga gajiyayyu da marasa aiki.

Taron ya samu halarcin baƙi na kusa da na nesa ciki har da manyan jami’an gwamnati da kuma ‘yan siyasa.