Da yiwuwar mace ta yi gwamna a Kaduna, inji El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa, yana da yaƙinin cewa, mace za ta iya ɗarewa kujerar gwamna a jihar duba da yawan mata a Kadunan.

Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a Kaduna a ranar Talata, El-Rufai ya ce mata su na da damar yin gwamna har kashi 50 cikin 100 duba da cewa sune su ka kwashi rabin al’ummar jihar.

El-Rufai, wanda mataimakiyarsa mace ce, Hadiza Balarabe, ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa mata damarmaki daidai da maza.

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa na da manyan kwamishinoni mata.

Ya ƙara da cewa shi ya na ganin bai wa mata dama daidai da maza yana sa su riƙa yin ƙwazo, wani lokacin ma sama da mazan.

El-Rufai ya kuma yi kira ga sauran gwamnatocin jiha da su riƙa bai wa mata damarmaki, inda ya ce “hakan zai ƙara ciyar da ƙasar nan gaba”.

Gwamnan ya ce jihar na fatan ta samu nagartaccen shugaba da zai ɗora daga kan kyawawan ayyukan da yake yi.