
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ce babu wanda ya mutu a yayin gobarar da ta kama wani sashi na otal ɗin da alhazan Nijeriya guda 484 suke zama a Makkah.
Mataimakiyar daraktan yaɗa labaran NAHCON, Hajiya Fatima Usara ta bayyana hakan a wata takarda, ranar Lahadi.
Ta ce, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na ranar Asabar a ‘Imaratus Sanan Hotel’ a lokacin da mahajjatan suke gudanar da ibada a Mina.
Tuni hukumomin Saudiyya da haɗin-gwiwar hukumar gudanarwar otal ɗin suka kai ɗauki na gaggawa tare da kashe gobarar, lamarin da ya dakatar da cigaba da yaɗuwarta zuwa sauran sassan ginin.
Ta kuma ce, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh ya ziyarci wajen da abin ya faru domin ganin matakin ɓarnar tare da tabbatar da ɗaukar matakan kulawa ga alhazan.
Daga nan ne Farfesan ya kuma umarci a gaggauta sauya wa alhazan masauki tare da samar da musu da wasu ababen da suke buƙata.
Kazalika, ya yaba wa hukumomin gaggawa na Saudiyya da haɗin kan jami’an hukumar gudanarwar otal ɗin wajen daƙile iftila’in.
