
Daga BELLO A. BABAJI
Mutum ɗaya ya rasa ransa a yayin da wasu biyu suka jikkata a sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai wa masallata da ke tsaka da sallar Isha a Ƙauyen Moriki dake Gundumar Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
Bayanan sirri daga ƙwararre kan sharhin dabarun daƙile ta’addanci, Zagazola Makama, ya ce harin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Asabar a lokacin da maharan suka farmaki jama’a a ƙauyen, inda suka yi ta harbe-harbe a wani ƙaramin masallaci.
Ganin hakan ne ya sa aka baza jami’an tsaro a yankin da nufin daƙile harin da kuma ƙoƙarin kwantar da hankulan al’umma a yankin.
Tuni aka garzaya da mutane biyun zuwa asibiti, yayin da aka miƙa gawar wanda ya rasu ga iyalansa domin yi masa jana’iza.
A wani labarin, ƴan bijilante da ke aiki da dakarun tsaro na Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda guda uku da kama wani gami da ƙwato babur biyu a Ƙaramar Hukumar Maru dake jihar.
Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 3:00 na rana a lokacin da ƴan bindiga huɗu akan babura suke ratsawa ta ƙauyukan Ƴan Mangwarora, Mallamawa da Kurar Mota a Gundumar Ɗan-Sadau.
