NAF ta tarwatsa maɓoyar ƴan ta’adda a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Rundunar sojojin sama (NAF) sun yi nasarar tarwatsa maɓoyar ƴan ta’adda a Jihar Borno.

NAF ta ce, harin, wanda ta kai ta sama ya yi sanadin tarwatsa wasu mafaka na ƴan ta’adda da daƙile harin da mayaƙan suka shirya kaiwa a ranar sallah a jihar.

Kakakin NAF, Air Kwamado Ehimen Ejodame a wata takarda ya ce dakarun sun kai harin ne a ranakun 5 da 6 ga Yuni, 2025.

Takardar ta bayyana cewa dakarun na Atisayen HAƊIN KAI sun lalata maɓoyar Boko Haram a yankin Tumbumma Baba da Chiralia dake kudancin Tumbuns a jihar.

Ya ce, jiragen jami’an ya hari inda mayaƙan ƴan ta’addar suka shirya kai hari da wajen ajiyar makamansu bisa samun wani rahoton sirri da ke bayyana yadda aka shirya haddasa tashin-tashina a yayin bukukuwan sallah.

By Babaji