Trump ya sanya motarsa ta kamfanin Tesla a kasuwa kan rashin jituwa da Elon Musk

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Donald Trump na shirin sayar da motar Fadar White House ta kamfanin Tesla a yayin da dangantakarsa da Elon Musk ta yi tsami.

A watan Maris ne Trump ya sayo motar mai ƙirar ‘Model S Tesla’ a lokacin da Musk ya gabatar da ita a fadar.

Trump ya sayi motar ne da nufin haɓaka kasuwancin Musk a lokacin da matakin raba hannun-jarin kamfanin nasa ya yi ƙasa.

Saidai, wani babban jami’i ya shaida wa NewsNation cewa Trump na shirin sayar da motar ko kuma kyautar da ita duba da rashin jituwarsu, wadda aka ajiye ta White House kuma ma’aikata suke amfani da ita.

Musk ya kashe ɗaruruwan miliyoyin daloli a yayin zaɓen Shugaba Trump a karo na biyu kuma ya samu muƙami a gwamnatin.

Amma daga bisani an samu tsaiko a alaƙarsu a lokacin da Trump ya gabatar da ƙudirin haraji da kashe-kashe.

By Babaji