Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙaramin ministan tsaro Hon Bello Mohamed Matawalle ya ƙalubalanci gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal kan ikirarin da ya yi cewa ya gaji kuɗi a baitul malin jihar miliyan huɗu kacal daga gwamnatin da ta gabata ta Matawalle a shekarar 2023.
Ministan ya bayyana cewa ya bar Naira biliyan 49 a baitul malin jihar lokacin da ya miƙa ragamar mulki ga gwamna Dauda a shekarar 2023.
Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin magoya bayan jam’iyyar APC daga shiyyar Zamfara ta yamma da suka kai masa ziyarar barka da Sallah a gidansa da ke garin Maradun hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun a yau Lahadi.
Ya bayyana ikirarin da gwamna Dauda ya yi a matsayin soki burutsu da siyasa da nufin ɓatawa jam’iyyar APC da suna a idon Duniya.
Matawalle ya ce ya yi duk mai yiwuwa don ganin an samu jin daɗin jama’a a lokacin da yake riƙe da muƙamin gwamnan jihar musamman a fannin tsaro da gudanar da mulki baki ɗaya domin ci gaban jihar.
Matawalle ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta baiwa sojoji dukkanin kayan aikin da ake buƙata domin yaƙi da ‘yan ta’adda da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Ya kuma tabbatar wa manoma a yankin Arewa maso Yamma da faɗin Nijeriya, cewa za su koma noma a wannan damina, inda ya ce sojoji na aiki ba dare ba rana domin daƙile ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.
Ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC a jihar da su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya tare da bin doka da oda don samun Nasarar shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 .
