Gwamna Abba a kan sikeli bayan shekaru biyu

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Waiwaye adon tafiya, in ji Malam Bahaushe. Yau shekaru biyu ke nan cif da dare karagar Mulkin Kano a matsayin Gwamna, kuma mahimmin lokaci na tsayawa a dora Gwamna a sikeli domin tantance ko ya cika alkawarin da ya yi rantsuwa a kai ko kuma ya gaza? Domin haskawa Kanawa su gane shin lokacin a yi masa tafi ne da san-barka ko kuma na tunasar da shi ya sake zage damtse idan ya na bukatar cika alkawarin da ya dauka da kuma neman zarcewa a kan wannan kujera.

Kowa ya san yadda Abba Gida-Gida ya yi matukar farin jini a wajen matasa tun daga zaben 2019, wanda ya kama hanyar lashewa, kafin a soko Inconclusive a kayar da shi. A 2023 farin jininsa ba ga yan Kwankwasiyya kadai ba, har mu yan jarida mun goya masa baya domin aikinmu a kullum tsayawa ne kan a yiwa al’umma adalci wajen ganin an yi musu abinda su ke bukata, kuma ganin yadda gwamnatin Ganduje ta kaucewa wannan tsari muka goyi bayan canji.

Abba ya shigo gwamnati da fatan alheri ba na kanawa kadai ba, har daga wasu sassa na Arewa da Najeriya. Amma abin takaici shine tashin farko sai ya kasance babban aikin da ya sa a gabansa shine na rusau. Rusau mafi girma a tarihin Najeriya wanda ya janyo asarar dukiya da aka kiyasta ta kai Naira biliyan 126. Ko kun san cewa a shekarar 2023 gwamnatin Kano ta tara harajin cikin gida biliyan 40 ne kacal? Amma ta yi rusau ninki uku na Hakan? Sannan ta tara biliyan 80 a kudaden shiga na cikin gida a shekarar 2024, wanda idan ka hada da waccan jumla da ta tara a 2023, wato a shekaru biyu, shine fa daidai da rusau din da ta yi a wata guda. A shekarar 2023 dai, gaba dayan abinda ta karba daga gwamnatin tarayya biliyan 125, shi ma kun ga kasa da abinda aka rushe ne. Kuma a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai, abinda ya gurgunta tattalin arzikin kasar gaba daya. Shekarar farko kenan wadda a sakamakon wannan rusau da fusata wasu Yan siyasa ya janyo aka yi ta kai ruwa rana a kotunan kasa kama daga Tribunal, Appeal Court har zuwa Supreme Court. 

Daf da sanarwar hukuncin kotun koli, akasarin mutane, har da ni, cikinmu ya duri ruwa a zaton cewa Supreme Court za ta tabbatar da Gawuna a matsayin Gwamna, domin har rubutu nayi na baiwa mutane hakuri idan hakan ta kasance. Amma da yake Allah ne mai yadda ya so, sai ga shi an tabbatar da Abba a matsayin wanda zabensa ya tabbata. Mutane sun yi matukar farin ciki, kuma ana ganin wannan zai sakar masa mara ya bude ayyuka. 

Amma maimakon bayan samun wannan nasara daga Allah, mu ga gagaruman ayyuka na ci gaban jihar Kano, kwatsam sai ga sabuwar dokar majalisa ta mayar da Sunusi Lamido karagar Sarkin Kano. A tarihin jihar Kano tun daga kafa ta, ba na jin akwai abinda ya raba kan kanawa, ya jawo mana zagi da raini da zub da mutunci irin wannan dambarwar ta masarautar Kano. Yan siyasar mu (Gwamna, Kwankwaso da Ganduje) tare da Sarakunan guda biyu, dukkansu ba su yiwa Kanawa adalci ba, domin sun bi son ransu fiye da martabar masauratarmu da tayi shekaru sama da dubu. Yau an wayi gari babu wani Sarki cikin biyun da ba a muzanta shi ba a titi, kowannensu kimarsa ta zube warwas a wajen daya bangaren da kuma mutane a sassan Duniya.

Daf da cika shekaru biyu a kan mulki, hankalin gwamnati da na mutane ya karkata ga yadda za’a kalli nasara ko akasin wannan gwamnati ta kwankwasiyya. Za ka ga ana ta yada cewa #Abbaisworking (wato Abba na aiki) hakika Abba na aiki, idan ka duba yadda ake ta Gina gadojin sama, fentin wuraren gwamnati, saka fitilun titi, da shimfida kwalta a wasu wurare. A ayyuka mafi girma na kudade da ta bayar a nan kusa shine na kwangilar sake gina majalisar jihar a kan biliyan 40. Sannan a baya ta bada kwangilar gina gadojin sama da aka kiyasta a kan Naira biliyan 27. Lokacin da aka bada wannan aiki na yi maƙala me taken “Shin Kanawa na bukatar gadar sama a yanzu?” domin idan ka yi la’akari da durkushewar tattalin arzikin kasa da yadda rusau ta janyo tsaiko a kasuwanci, da talaucin da ka jefa mutane, shin ya kamata a saka wadannan makudan kudade don sake gina majalisa, ko Gina gadojin sama? Kar mu manta idan ka zana Da’ira (circle) wanda ta hado da wadannan gadoji a ƙwãryar birnin Kano, za ka samu akalla gadoji sama da guda 10.

A irin wadannan ayyuka dai, gwamnati ta bada kwangilar biliyan daya a saka wutar Solar a gidan gwamnati, da kashe sama da miliyan 500 don yiwa ofishin sakataren gwamnati kwaskwarima. An kuma sake farfado da ayyukan kilometer biyar na kananan hukumomi wanda a kason baya bayan nan zai lakume biliyan 20. Naga har wani babban malamin Jami’a mai matukar kima sosai ya fito ya ke cewa hakika Abba na aiki tare da kawo irin wadannan misalai. Abin tambaya a nan shine, tsakani da Allah irin wadannan ayyuka kacokan ya kamata a ce ana ta kashe kudadenmu a kai? A jihar da:

1. Ruwan sha me kyau ya gagari kaso 39% Kuma kaso 51% ba su da matsuguni Mai tsafta?

2. Jihar da ke da almajirai miliyan 1.6 na gararamba a tituna babu isashen abinci?

3. Jihar da mutane sama da miliyan 1.2 ba su da tartibin aikin yi?

4. Jihar da ke da Dam 22 su na barci ba noman kifi da tumatir da sauransu?

5. Jihar da a duk mata dubu goma 57 ke mutuwa wajen haihuwa saboda karancin kula da haihuwa.

6. Jihar da a duk haihuwa dubu, jarirai 103 ke mutuwa.

7. Jihar da ke da likitoci 1300 domin kula da mutane miliyan 20 (likita guda ga marasa lafiya 11,500).

8. Jihar da a kullum ake haihuwar mutane 1000 a Rana (wato mutane 30,000 a wata) me ake musu tanadi?

9. Jihar da Kaduna ta bige ta a wajen tara harajin cikin gida?

Hakika wannan matsaloli ba a wannan gwamnati su ka sami asali ba, gwamnatocin baya na da laifi sosai saboda gazawarsu a wadannan bangarori. Amma magana ta gaskiya ita ce, mun tsammaci gwamnatin Kwankwasiyya idan ta shigo zata maida hankalinta a kan irin wadannan matsaloli da suka shafi talaka ta fara shawo kansu. Amma abin takaici sai ya zama jiya-i-yau tamkar abinda bature ke cewa “Old wine in a new bottle”.

Babu gwamnati a tarihin Kano da ta sami kudade a shekaru biyu irin wannan gwamnati domin a 2023 an sami FAAC Biliyan 125 da IGR Biliyan 40, sannan a 2024 an sami FAAC Biliyan 200 da IGR da aka tsammata na Biliyan 80 sai a wannan shekarar ana tsammatar FAAC na Biliyan 531 da IGR na Biliyan 100. Wato a jumlace zuwa karshen wannan shekara ana sa ran jihar Kano daga 2023 zuwa 2025 za ta saka a lalitar ta, Naira Tiriliyan 1 da biliyan 70. Shin baya ga kyale-kyale na tituna da gadoji da fenti da fitulu a ƙwãryar birnin, ina za a ga wadannan makudan kudade da aka samu? Shin sun kawo dauki a harkar ruwan sha, asibitoci, makarantun firamare, noma da samar da ayyuka ga matasa? Ko kudaden al’umma na yan siyasa ne kadai da ma’aikatan gwamnati banda talakawa?

A karshe mu na kira ga wannan gwamnati, a matsayin mu na masu bibiyar al’amura ba adawa ba, da ta sauya salon yadda ta ke kashewa al’umma kudadenta, ta hanyoyin da ba su ake matukar bukata ba. Misali na na karshe shine a makon da ya gabata, gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 6.8 domin gina sabon Dam na Dansoshiya a karamar hukumar Kiru. Ya ilahi Kano da ke da Dams 22 wadanda akasarinsu barci su ke yi, domin hatta na Tiga mafi girma a jihar, kaso 40% cikin 100% kacal ake iya amfana tsawon shekaru 50. Sannan akwai Dams akalla guda Tara da su ka yiwa Kiru kawanya, wato Dams din Bagwai, Tomas, biyu a Kazaure (duk da na jihar Jigawa ne wadannan) da guda hudu a kan titin Kano zuwa Gwarzo. Don me ba za a saka kudin wajen raya wani daga cikin wadannan Dams ba, za a sake Gina sabo? Me ake da wadancan 22?

Mutane na yiwa wannan gwamnati kyakkyawan fata tun shigowarta, kuma lokaci ya kusa kure mata. Idan ba a yi abinda ya kamata ba, nan ba da dadewa ba, za a yi da-na-sani. Muna fatan Allah ya basu ikon gyarawa domin amfanuwar al’umma gaba daya. Domin a zangon shekara biyu, hakika nauyin sikelin Abba, bisa dogaro da wadancan alkalumma, bai karkata zuwa inda bukatun mutane na hakika su ke ba, ya karkata ne ga inda bukatun masu mulki su ke kawai, kuma Kanawa na nan su na kallo, kafin 2027.

Malam Ali ya aiko ne daga Kano

By ukarofi