Daga HASSAN IMRAN
A makon da ya gabata, Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya ta gudanar da bikin cika shekaru sittin da ɗaya da kafuwa. Rundunar sojojin sama ɗaya ce daga cikin rundunonin tsaro masu tabbatar da kariya da zaman lafiya a ƙasar nan. Abu ne da muka sani cewa zaman lafiya da fahimtar juna ba za su taɓa samuwa ba har sai ‘yan ƙasa sun bada tasu gudummawar. Wannan gudummawar za ta ƙarfafa alaƙa tsakanin farar hula da sojoji ainun. Haka zalika, za ta inganta sha’anin tsaro kuma za ta ƙarfafa gwiwar jami’an tsaron a duk inda suke.
Alaƙa tsakanin farar hula da sojoji tana nufin ƙulla alaƙa wacce za ta tabbatar da tsaro da cigaban al’umma, a duk inda jami’an tsaron suka yada zango, ko kuma duk inda aikin tsaro ya kai su. Wannan alaƙar ta ƙunshi son juna, kau da idanu da kuma nuna tausayi ga juna. Wannan na nufin cewa kowanne a cikin mu yana da tasa gudummawar da zai bayar domin tabbatar da tsaro a ƙasarmu.
Daga cikin hanyoyin da za mu taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin farar hula da sojoji akwai;
Hanya ta farko, taimaka masu da bayanan sirri. Bayanan sirri na ɗaya daga cikin mafi girma ginshiƙin tsaro kuma wata hanya ta samun nasara a kowanne aiki (operation) da sojoji suka fita. Farar hula su ne suka san nagari da ɓatagari a yankunansu. ɗaukar ƙara zuwa ga jami’an tsaron akan wani abu ko kuwa harkokin da suka saɓa doka zai taimaka wa dakarun wajen daƙile fargaba da tashe-tashen hankula a yankunanmu.
A makon da ya gabata, akwai wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, game da wasu samari ‘yan Arewa waɗanda aƙalla adadin su ya kai tamanin da aka gani suna tsaye a gaban ginin kamfanin Dano dake Ibeju-Lekki a garin Legas. Al’ummar garin sun kai ƙara ga hukumar ýansanda ta Jihar Legas. Nan take suka tura da jami’an su domin binciken waɗannan samarin. A binciken da suka gudanar sun gano cewa waɗannan samarin daga Jihar Katsina suke, kuma an ɗauke su aiki ne a matsayin leburori a matatar mai fetur ta ɗangote.
Wannan matakin da ‘yan garin suka ɗauka haka ya kamata mu riƙa yi a Arewa a duk lokacin da muka ga wata baƙuwar fuska a unguwannin mu ko kuma muka ga wani mutum na wasu zagaye-zagaye ko zirga-zirgar da ba mu yarda da ita ba. Mu sani cewa shi lamarin tsaro abu ne da ya shafi kowa. Jami’an tsaro ba za su iya yi ba su kaɗai dole sai mun taimaka masu da bayanan sirri. Abin da ya ƙara ingiza garkuwar da ake da mutane da kuma ta’addanci da kashe-kashen babu gaira babu dalili shi ne domin mun bar harkar tsaro a hannun gwamnati da jami’an tsaro kaɗai, ba tare da ba da tamu gudummawar ba.
Ya zama dole mu farar hula mu taimaka wa jami’an tsaro wajen bayyana ɓatagari ko ɗan ta’addan da ke cikin unguwanninmu ga jami’an tsaro. Mu sani cewa ba daidai ba ne ɓoye ɓatagari ko ɗanta’adda, domin ƙabilar mu ɗaya da shi, ko kuma addinin mu ɗaya.
Hanya ta biyu, mu kiyaye nuna ƙabilanci a dukkan harkokinmu. ƙabilanci wata hanya ce ta tunani ko halayen da wasu mutane ke fifita da nuna goyon baya ga ýan’uwansu da ke ƙabila ɗaya ko suke amfani da harshe ɗaya, ba tare da la’akari da cewa, abin da suke goyon baya daidai ne ko ba daidai ba. Kuma ko ya dace da dokokin ƙasa, da nuna kishi ga kasarsu. ƙabilanci ya shiga mana zukata har hakan ya kawo taɓarɓarewar sha’anin tsaro. Sau da yawa, mutane na ɓoye ɓatagari domin mai laifin ɗan yarensu ne, ko kuma addininsu ɗaya.
Abin takaici ne da ban haushi, sau da yawa ba ma taimakawa juna ko ɗaukar juna a aiki face mun bincika daga wanne yanki mutum yake? Wacce ƙabila ya fito? Ko kuma wanne yare yake yi? Wasu lokuta har tambaya muke yi mene ne aƙidarsa? Shin ɗan izala ne, ko ɗan ɗariƙa ne? Ko ɗan Shi’a ne? Wannan halayya ta nuna bambanci da wariya sun janyo mana matsaloli da yawa a ƙasar nan, kamar rashin haɗin kai, ƙiyayya da gaba da rikice-rikice da sauransu.
Manzon Allah (SAWA) ya yi mana gargaɗi mai tsanani akan nuna ƙabilanci inda yake cewa, “Duk wanda ya yaɗa da’awar ƙabilanci ba ya tare da ni gobe al-ƙiyama. Haka zalika, duk wanda aka kashe shi yana kare muradun ƙabilanci ba ya tare da al’ummata. Sannan, duk wanda ya mutu yana riƙe da aƙidar ƙabilanci ba ya tare da al’ummata gobe ƙiyama.’
Mu sani cewa, ba ya daga cikin ƙabilanci mutum ya so jiharsa ko kuma ‘yan ƙabilarsa. Manzon Allah (SAWA) ya fayyace mana abin da ake nufi da ƙabilanci, yayin da wani Sahabinsa ya yi masa tambaya kan cewa, ‘Shin yana daga cikin ƙabilanci mutum ya so ƙabilarsa?’ Sai Ma’aiki (SAWA) ya amsa da cewa, ‘A’a, ƙabilanci mafi muni shi ne mutum ya taimaka wa ‘yan ƙabilarsa akan zalunci.’
Hanya ta uku, ƙarfafa alaƙa ta ‘yan’uwantaka a tsakanin mu ‘yanƙasa, waɗanda Allah Ya ƙaddara rayuwarmu da zama a Nijeriya. Abu na biyu da Manzon Allah (SAWA) ya tabbatar da shi bayan gina masallaci a garin Madina lokacin da ya yi hijira, shi ne ƙarfafa alaƙa tsakanin mutanen Makka da na Madina. Ya sulhunta ‘yan ƙabilar Aws da ‘yan ƙabilar Khazraj bayan sun kasance abokan gaba gabannin zuwan Manzon Allah (SAWA). Ba sa aurar junansu kuma ba sa cin abincin juna, domin tsananin ƙiyayyar dake tsakanin su. Amma sulhun da Manzon Allah ya yi musu ya sanya suka zaman ýan’uwan juna. Haka zalika, Manzon Allah (SAWA) ya ƙarfafa alaƙa tsakanin Yahudawa da Kiristoci da suke garin Madina, domin tabbatar da tsaro da lumana.
Abu mafi muhimmanci ga ‘yan Nijeriya shi ne mu riƙa ganin junanmu a matsayin ýan’uwa. Dukkanin mu jikokin Annabi Adamu ne. Mu sani cewa babu wata ƙabila da tafi wata. Kuma a kowacce ƙabila akwai nagari da mugu. Mu mayar da hankali akan abinda ya haɗa mu fiye da abinda ya raba mu. Dukkan mu ýan Nijeriya ne kuma tunda Allah ya haɗa mu tare sai mu zauna lafiya da junanmu. Mu bada ƙarfin gwiwa akan dukkan abinda zai kawo mana cigaba a ƙasarmu.
Hanya ta huɗu, ita ce taimaka wa dakarun mu da addu’o’i. Sojojin Nijeriya na bada kyakkyawar gudumawa wajen cigaban al’umma da kuma ƙasarmu. Suna hana idanunsu barci domin kare rayukan mu da dukiyoyin mu. Daga cikin ribar ayyukansu; mutane zasu iya gudanar da addinin su ba tare da wani tsoro ba, ‘ya’yanmu za su je makarantu da jami’o’i domin nema ilimi, ba tare da wata fargaba ba. Haka zalika, kasuwanci da sana’o’i za su gudana ba tare da wani tashin hankali ba. A yayin da suke kare mana rayuka da dukiyoyinmu wasu na rasa rayukansu a filin daga, wasu kuma na ɓata. Waɗansu kuma na jin rauni da har abada baza su rabu da shi ba. Don haka, inda ba za mu yabi sojojin Nijeriya ba, bai kamata mu zage su ba.
Addu’ar mu ga sojojin mu za ta kawo masu nasarori a dukkan harin da suka kai wa ýan ta’adda da kuma masu tada zaune tsaye. Babu wata rundunar da Manzon Allah (SAWA) ya shirya da za ta fuskanci abokan gaba a filin daga ba tare da Manzon Allah (SAWA) ya yi masu addu’a kuma ya umurci a taimaka masu da addu’a ba.
Muna roƙon Allah Ya kawo mana wadataccen tsaro da zaman lafiya a ƙasar mu, kuma Allah Ya kawar da duk ayyukan ýan ta’addan ya kuma bai wa dakarun mu nasarori masu yawa, a duk inda suka kasance. Amin.
Malam Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected]
