Balaguron Buhari: ‘Ba sai Buhari ya miƙa wa Osinbajo ragamar mulki ba’, Fadar Shugaban Ƙasa

Daga FATUHU MUSTAPHA

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa ba lallai ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ba, don ya tafi dubar lafiyarsa a ƙetare.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar Channels a Talatar da ta gabata.

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari bai saɓa wata doka ba na rashin miƙa wa mataimakinsa ragamar mulkin ƙasa alhalin ya bar ƙasa na wasu ‘yan kwanaki.

Yana mai cewa, “Shugaba Buhari zai ci gaba da gudanar da harkokinsa daga inda yake.”

Ya ƙara da cewa abin da dokar ƙasa ta tanada shi ne, “Idan Shugaban Kasa zai bar ƙasa na tsawon kwana 21 ko fiye da haka, sai ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa, amma a irin wannan hali babu buƙatar hakan.”

Buhari ya tafi Ƙasar Landan ne domin duba lafiyarsa inda ake sa ran dawowarsa ya zuwa mako na biyu na watan Afrilu, in ji Fadar Shugaba Ƙasa.