Ballon d’Or 2022/23: Messi da Haaland sun shiga jerin ’yan takara 30

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mujallar Faransa ta fitar da sunan ‘yan wasa 30 da ke takarar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa, wato Ballon d’Or na duniya na 2022/23.

Cikin ‘yan wasan har da Lionel Messi da Erling Haaland, waɗanda ake hasashen wani daga ciki ka iya lashe kyautar.

Wasu ‘yan wasan da suka taka rawar gani da ake ganin za su iya lashe kyautar sun haɗa da Vinicius da Rodri ko kuma Kevin de Bruyne.

Tsohon ɗan wasan Real Madrid, wanda ya koma taka leda a babbar gasar tamaula ta Saudiyya, Karim Benzema, shi ne gwarzon Ballon d’Or na bara.

Wannan karon za a auna ƙwazon ɗan wasa a kakar 2022/23, ke nan daga fara kakar a watan Agusta zuwa Yuli da aka kammala.

Saboda haka za a yi la’akari da gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, wanda hakan zai bai wa Messi damar lashe Ballon d’Or na takwas jimilla ke nan.

Sai dai duk da haka Haaland yana da damar lashe kyautar, bayan ƙwallayen da ya ci a kakar da ta wuce da ɗaukar gasar Firimiyar da FA Cup da kuma gasar Zakarun Turai.

Messi, kyaftin ɗin Argentina, wanda yanzu ke taka leda a Inter Miami ya ci ƙwallo bakwai da bayar da uku aka zura a raga daga 15 da Argentina ta zura a raga ta lashe kofin duniya a Qatar.

Da ma dai shi ne kaɗai kofin da tsohon ɗan wasan na Barcelona da Paris St Germain bai ɗauka ba a baya, yanzu ya haɗa dukkan wani babban kofi a fannin tamaula a duniya.

Messi bai yi ƙwazo ba sosai a PSG, amma ya taka rawar gani a 2021, wanda bai ɗauki gasar Zakarun Turai ba, amma ya lashe Ligue 1 a ƙungiyar.

Shi kuwa Haaland, wanda ya fara kakar farko a bara a Premier League tare da Pep Guardiola ya ci ƙwallaye da yawa da lashe Premier da FA Cup da kuma Champions League.

Haaland ya zama kan gaba a cin ƙwallaye da yawa a Premier League da lashe takalmin zinare da zama fitatcen ɗan ƙwallo a Turai a bara.

A kakar da ta wuce Haaland ya zura ƙwallo 52 a raga a karawa 53 a dukkan fafatawa, wanda yanzu ya ci ƙwallo shida a wasa hudu a Premier League.

’Yan wasa 30 da ke takarar Ballon d’Or na 2022/23:

Karim Benzema
Josko Gvardiol
Jamal Musiala
Andre Onana
Mohamed Salah
Bukayo Saka
Kevin de Bruyne
Jude Bellingham
Kolo Muani
Bernardo Silva
Khvicha Kvaratskhelia
Nicolo Barella
Emiliano Martinez
Ruben Dias
Erling Haaland
Martin Odegaard
Ilkay Gundogan
Yassine Bounou
Julian Alvarez
Vinicius Junior
Leo Messi
Rodri
Lautaro Martínez
Antoine Griezmann
Robert Lewandowski
Kim Min-jae
Luka Modric
Kylian Mbappe
Victor Osimhem
Harry Kane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *