Gwamnatin Buhari ta ɗaiɗaita tattalin arzikin Nijeriya – Khalifa Sanusi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya ce tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gurgunta tattalin arziki ba tare da neman shawarar ƙwararru ba.

Sarki Sanusi wanda kuma shi ne tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana hakan a wani saƙon bidiyo da ya aike wa ‘yan Nijeriya ta yanar gizo.

Ya bayyana cewa wasu sun ribaci riƙon sakainar kashi da aka yi wa tattalin arzikin da har aka samu “wani yaro mara ilimi” ya mallaki jirgin sama a ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe.

Ya buqaci ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri da wannan gwamnati da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta, yana mai cewa gwamnatin baya ce ta gurgunta komai.

Sanusi ya bayyana cewa an sha samun masu rubuto masa takarda suna neman ya yi magana kan halin da ƙasar nan ke ciki.

Sai dai ya ce wannan ba lokaci ba ne da ya kamata ya yi magana kan matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

“Shekara takwas da ta wuce, Nijeriya ta yi rayuwar ƙarya, gwamnati ta ciyo bashi daga ciki da wajen ƙasar nan. Kimanin Naira tiriliyan 30 aka karɓo daga Babban Bankin ƙasar.

“Duk kuɗaɗen shiga da ƙasar nan ta samu a cikin ’yan shekarun da suka gabata ba za a iya biyan bashi ba. Bashin ya wuce kashi 100.

“Waɗanda suka rubuta takarda, suna neman mu yi magana kan halin da ƙasar nan ke ciki; amma bai dace in yi magana a yanzu ba.

“Kamar direban da ke kan hanya yana tuqi da ganganci ne ka ja hankalinsa game da rami a gaba bai saurare ka ba. Me za ka faɗa masa bayan motar ta faɗa cikin rami?

“Mutane sun qi sauraron mu a lokacin. Yanzu za mu ba su shawara kawai su yi haƙuri. Ba zan tava cewa Tinubu ya ingiza Nijeriya cikin wahala ba. Ba wai ba shi da aibu ba ne.

“Idan sun qara haraji, dole ne mu biya tun da rancen kuɗi ba zai yiwu ba. Idan CBN ya buga ƙarin takardun Naira, dala za ta kai Naira 1,500. Dole ne mu sha wahala. Lokacin da nake Gwamnan CBN duk dala ɗaya ana canjar da ita N150 ne. A yau kuwa ta kai kusan N900.

“Sun yi wa tattalin arzikin abin da suke so kuma sun ƙi sauraron masana.

“A cikin shekara takwas da ta gabata kawai shafaffu da mai sun sayi dala a kan N400 sannan suka sayar da N540.

“Akwai yaron da ba shi da gogewa kuma wanda bai taɓa yin aiki a ko’ina ba ya mallaki jirgin sama mai zaman kansa.”