Ban san makomata ba a Man City – De Bruyne

Kevin De Bruyne ya ce, bai san makomarsa ba a kakar nan a Manchester City, bayan da aka dakatar da batun tsawaita masa kwantiragi.

Yarjejeniyar mai shekara 33, za ta kare a ƙarshen kakar nan, kuma an tsayar da batun tsawaita masa a lokacin da yake jinya daga raunin da ya ji cikin Satumba.

Wasa tara ya buga kawo yanzu, amma ya canji ɗan wasa a karawa uku da Man City ta yi a bayan nan a shirin da yake na koma kan ganiya.

”Na kwan da sanin cewar da fara kakar nan, zan tattauna da mahukunta don fayyace makomata, sai kuma na ji rauni a wasa da Brentford daga nan aka jingine batun,” inji De Bruyne.

”Na yi fatan yin jinyar kwanaki, amma sai na ɗauki mako takwas zuwa tara, amma yanzu fatan da nake na koma kan ganiya, sannan na ga abinda zai biyo baya.

De Bruyne ya ƙara da cewa, ya tattauna da mahukuntan kan makomarsa a bara, amma baya cikin yanayin da ya dace ya ci gaba da tattaunawar, bayan raunin da ya ji.

Dan wasan tawagar Belgium ya koma City daga Wolfsburg mai buga Bundesliga a 2015 kan yuro miliyan 55.

Kaka ɗaya tsakani Pep Guardiola ya koma Etihad da horar da tamaula, wanda ya sauya gurbin da De Bruyne ke taka leda.

Tun kafin fara kakar nan an yi ta alakanta kyaftin ɗin tawagar Belgium da cewa zai koma taka leda a babbar gasar tamaula ta Saudiyya.