Leicester City ta kori kocinta, Stave Cooper

Kungiyar Leicester City ta kori mai horas da ’yan wasanta Stave Cooper daga aikinsa.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi ta ce, a yanzu Ben Dawson ne zai amshi jagorancinta a matsayin mai horarwa na riƙon kwarya, kafin naɗa sabon mai horaswa.

Korar ta Cooper da Leicester ta yi dai, ya biyo bayan rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a hannun Chelsea ci 2-1 a filin wasa na Power King.

A yanzu dai ƙungiyar Leicester City na a mataki na 16 a gasar firimiyar Ingila, bayan buga wasanni 12 inda take da maki 10 kacal.

Kungiyar ta tsorata da salon jagorancin Cooper ne, wanda ake ganin idan har aka ci gaba da tafiya a haka, ba zai iya samar mata da gurbin ci gaba da zama a gasar firimiyar Ingila a kakar wasa ta shekara mai zuwa ba.