Madrid ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona a La liga

Real Madrid ta rufe tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona da ke a saman teburin gasar La liga, bayan da ta je har gida ta lallasa Leganes da ci 3 da nema. 

Kylian Mbappe ne ya fara jefa ƙwallo a raga tun kafin aje hutun rabin lokaci, wacce itace ƙwallo ta 7 da ɗan wasan ya jefa a gasar La liga a bana.

Bayan dawowa hutun rabin lokacin ne kuma Faderico ɓalɓerde ya ƙara ƙwallo ta biyu a wani bugun tazara da suka samu, kafin daga bisani a minti na 85 Jude Bellingham ya jefa ta uku.

Leganes wacce bata taɓa samun nasara a kan Madrid ba, a wasan na jiya ma bata samu damar kai koda hari ɗaya mai hatsari ba.

A yanzu dai tawagar ta Ancelotti ta koma mataki na biyu a teburin La liga, kuma tazarar maki 4 ne ke tsakaninta da Barcelona da ke jagorantar gasar, duk da cewa Madrid ɗin na da kwanten wasa ɗaya tsakaninta da Valencia.