Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankin Raya Afirka (AfDB) na shirin fara fitar da wani asusu na dala biliyan 2.2 don bunƙasa ayyukan noma a Nijeriya.
Darakta Janar na Ofishin AfDB na Nijeriya, Abdul Kamara ne ya bayyana haka a yayin bita na ƙarshen shekara ta 2024 na Channels Teleɓision mai taken, ‘Mayar da hankali kan fannin Noma, Tsaron Abinci, Bincike da Zuba Jari na AfDB’.
“Musamman daga shekara mai zuwa (2025), za mu ga an rattaba hannu kan kwangiloli kuma za a fara haɗa kai da wasu jihohi. Tabbas ba dukkan jihohin za su fara tare ba,” inji shi.
Ya ce, za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen bunƙasa cibiyoyin noma da masana’antu inda za a riƙa sarrafa su, da cibiyoyin hada-hadar kuɗi da kuma shirye-shiryen sauya fasalin noma.
Masanin tattalin arzikin ya ce, duk da cewa Hukumar AfDB ta amince da bunƙasa ayyukan noma na musamman a cikin 2021, aikin yana tasowa bayan jinkirin farawa saboda dalilai da yawa.
“Lokacin da kuka amince da shirin, dole ne ku sanya hannu da gwamnatin tarayya. Hakanan dole ne ku sanya hannu tare da masu haɗin gwiwa. Dole ne Bankin ya kawo IFAD (Asusun Cigaban Noma na Duniya) da Bankin Raya Musulunci a matsayin masu hada-hadar kuɗi,” inji shi.
