Bankin UBA zai fara harkokinsa a ƙasar Dubai

Daga AMINA YUSUF ALI

Bankin UBA ya faɗaɗa harkokinsa, inda har yanzu haka ya bude sabon reshensa a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (Dubai).

Shi dai wannan reshe na UBA an buɗe shi ne a cibiyar hada-hadar kuɗin ta qasar Dubai (DIFC). Sannan ya samu lasisin fara hada-hadar sa, kuma humakar saita al’amuran kuɗin na Dubai (DFSA), shi zai cigaba da gudanar da da al’amuran bankin.

Wannan faɗaɗa harkokinsa da bankin UBA ya yi ana ganin zai qara sa wa ya samu qarin damarmaki a gabas ta tsakiya, Afirka, da Asiya ta kudu, wanda ya ƙunshi ƙassashe 72 tare da ƙiyasin alumma wajen biliyan uku.

Wannan zai sa ya zama bankin Duniya wanda zai ba damar samun sauƙin cinikayya da hada-hadar kuɗin tsakanin ƙasashen Afirka da sauran ƙasashen Duniya.

A yayin da yake jawabi lokacin ƙaddamar da sabon reshen bankin a Dubai ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata, Shugaban rukunin bankunan UBA, Tony Elumelu, ya bayyana cewa, wannan ce rana da suka daɗe suna dako. Kuma a cewar sa, da sannu Bankin UBA zai zaga kowanne lungu da saƙo kuma tana kan gaba wajen kawo sauƙin kasuwanci a ƙasashen Afirka.

Hakazalika, shi ma manajan Daraktan UBA, Kennedy Uzoka, wanda ya yi jawabi shi ma taron, ya bayyana cewa, a yanzu haka bankin nasu yana da rassa a shiyyoyin Duniya guda huɗu sannan suna harkokinsu a ƙasashen Duniya guda 24 suna da abokan kasuwanci fiye da miliyan 35, kuma kullum abokan kasuwancinsu ƙaruwa suke yi.

Ya ƙara da cewa, UBA shi ne bankin Nijeriya na farko da ya samu qetarawa zuwa hadaɗɗiyar Daular Larabawa don kafa harkokinsa. Bayyanar Bankin a Dubai wata ‘yar manuniya ce a kan ingancinsu da shahararsu a faɗin Duniya.

Vikrant Bhansali, a halin yanzu dai shi ne shugaban sabon bankin UBA da ka bude a cibiyar hada-hadar kuɗin ta Dubai (DFIC).