Dalilin da ya sa Kano Pillars ta faɗi daga Firimiyar Nijeriya a bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ta tabbata cewar Kano Pillars ta faɗi daga gasar Firimiyar Nijeriya bana a karo na uku a tarihin ƙungiyar.

Tun farko ƙungiyar da aka kafa a 1990 ta faɗi daga gasar Firimiyar ƙasar a shekarar 1994 da 1999.

Ƙungiyar da ake kira sai masu gida wadda ta lashe kofin babbar gasar tamula ta Nijeriya karo huɗu ba za ta buga kakar da za a yi ta 2022/23 ba.

Ƙungiyar tana da daɗaɗɗen tarihi a fagen taka leda a ƙasar da Afirka, wadda ta samar da fitattun ‘yan wasa masu magoya baya da yawa.

Shugaban marubuta labarin wasannin ƙasa reshen jihar Kano, Zaharadden Saleh ya yi ƙarin bayani kan abubuwan da suka ja ƙungiyar ta faɗi a kakar bana.

Shugabancin Surajo Yahaya Jambul:

A shekarar 2019 gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Surajo Shu’aibu Yahaya da ake kira Jamul a matakin shugaban Kano Pillars.

Tun bayan da aka naɗa Jambul shugabanci wasu suka fara ƙorafin cewar bai da ƙwarewar jan ragamar babbar ƙungiyar kamar Pillars.

Wasu ma na ganin bai kamata tun farko a sauya Alhaji Tukur Babangida, wanda ya goge a sanin tamaular Nijeriya da ƙwarewa da gogewa ba.

Rashin sakin kuɗi daga gwamnati:

Gwamnatin jihar Kano ta janye daga bai wa Kano Pillars kuɗi kamar yadda aka saba yi, in banda albashin ‘yan wasa.

‘Yan ƙwallon suka koma ba sa samun ladan wasa da sauran kuɗaɗen da ke ƙara karsashin ‘yan ƙwallo domin suke saka kwazo.

Pillars ta buga wasanninta na gida a waje:

Sai masu gida ta koma buga wasa a Kaduna, filin da ake kira Ahmadu Bello daga nan ta koma karawa a Katsina, filin wasa na Muhammadu Dikko.

Daga nan ta koma wasa a Kano nan da nan ƙungiyar ta yi laifin da aka ɗauke ta zuwa Abuja, filin MKO Abiola na babban birnin tarayyar Nijeriya.

Kwashe maki shida daga Pillars:

Bayan da aka dawo da Kano Pillars buga wasa a gida wato filin wasa na Sani Abacha, an samu yamutsin fasa motar Katsina United cikin watan Afirilu.

An ƙara kwashe maki uku daga Kano Pillars kan laifin da Jambul ya aikata a karawa da Dakkada.

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nijeriya, LMC ta dakatar da shugaban Kano Pillars, Suraj Yahaya daga shiga harkokin wasanninta nan take.

Magoya baya sun taka rawar gani wajen faɗuwar Pillars:

Ƙungiyar magoya bayan Kano Pillars mai ɗimbin magoya ta bayar da gudunmawa wajen faɗuwar Pillars daga gasar Firimiyar Nijeriya a bana.

Magoya bayan sun ƙasa nuna halin ɗa’a a wasannin da ta buga a Kaduna da Katsina, wanda hukumar gudanar da gasar ta Nijeriya ke ta gargaɗinsu.

‘Yan wasan da Pillars ta dauka:

Ana ganin cewar Pillars ba ta ɗauki ‘yan wasan da suka da ce ba musamman a kakar nan, idan ba haka ba ya kamata su fahimci cewar sana’arsu ce ba wanda zai kama musu sai dai kwazonsu.