Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba – Masari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu gwamnatin Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba, ɗan bindigar da take nema ruwa a jallo duk da naɗin sarautar da aka yi masa a Zamfara.

Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ne ya shaida wa BBC cewar sun yi mamakin jin naɗin sarautar da aka yi masa, sai dai ya ce ko da a ce Ado Aliero ya daina ayyukan ta’adanci a Zamfara har yanzu a wajen su bai daina ba.

Ya bayyana cewa tun bayan faruwar wannan lamari, ya yi ƙoƙarin tuntuɓar Gwamnan Zamfara Bello Matawalle, amma bai same shi ba domin tattauna wannan batu.

Gwamna Masari ya ce har yanzu gwamnatin Katsina na kan bakarta ta neman Ado Aliero ruwa a jallo bisa zargin kashe mutanen Kadisau da kashe mutanen Faskari.