Tausayin maniyyata 700 ne ya sa ƙara’in zuwa Saudiyya bayan Arfa – Shugaban Hukumar Alhazan Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa tausayi da alhinin maniyyatan Nijeriya 700 da ba su samu zuwa aikin Hajjin bana ba, shi ne ya sa shugabannin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, kashi 90 cikin 100 na shugabannin ba su je aikin Hajjin bana ba, sakamakon matsalar rashin samun jirgi da Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta haddasa aiki a 2022 a cewarsa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano Farfesa Imam Sale Pakistan kuma, shugaban JIBWIS na Ƙasa reshen jihar Kano a lokacin da yake zantawa da manema labarai dab da zai jagoranci ayarin shugabanin hukumar jin daɗin alhazai ta jihar zuwa ƙara’in tafiya ƙasar Saudiyya bayan saukowa Arfa a Hajjin bana, a ranar Alhamis da ta gabata.

Farfesa Pakistan ya ce abin da ya faru ganin matsalolin da suka samu na saɓani da tangarɗar jiragen da za su kai maniyyatan Makkah da wahala da baƙin ciki da takaici da maniyatan na su suka samu a bana wanda hakan ta haddasa maniyyatan 700 ba su samu tashi zuwa aikin Hajji bana ba cikin 2,500 da suka samu guraben su na zuwa Hajjin bana, wanda matsaloli iri-iri suka faru da maniyyatan, domin a cewarsa wasu sun biya kuɗi shekara biyu amma saboda Korona ba a samu zuwa ba sai a wannan shekara ta 2022.

A ƙarshe ya ce, “abin da ya haddasa rashin samun zuwan maniyyata 4000 cikin dubu 43 da Nijeriya ta samu gurabensu a bana shi ne canza tsarin da NAHCON na da ta zo da wani sabon tsari da ya haddasa wannan matsala na rashin kwashe maniyyatan Nijeriya gaba ɗaya da NAHCON ce za ta tantance kamfanonin jiragen sama da za su yi aiki kuma hukumomin alhazai na jihohi ko wacce jiha ta zaɓa a ciki wanda hukumar hajji ta ƙasa, ta tantance amma bana ita ta tantance, ita kuma ta zaɓa wa jihohi da kanta, wannan shi ne ya haddasa matsala da ba ma fatan a maimaita ta kuma za mu bi haƙƙin alhazai ta hanyar da doka ta tanada,” inji shi.

By Editor