HOTUNA: Sanata Adamu ya cika shekara 76

Daga BASHIR ISAH

Jiga-jigan ‘yan siyasa daga ciki da wajen Jihar Nasarawa na ci gaba da miƙa saƙon taya murna na cika shekara 76 da haihuwa, ga Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi).

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule bai bari an baro shi baya ba wajen taya jigon siyasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bi shi har gidansa da ke Keffi ya miƙa masa katin taya murna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *